Gwamnatin Filato Ta Shawo Kan ’Yan Bindiga, Sun Mika Wuya Tare da Ajiye Makamai

Gwamnatin Filato Ta Shawo Kan ’Yan Bindiga, Sun Mika Wuya Tare da Ajiye Makamai

  • Gwamnatin jihar Filato ta ce ta yi nasarar cimma matsaya da wasu gungun 'yan bindiga a jihar kuma sun mika wuya tare da ajiye makamansu
  • Gwamnatin ta ce wannan nasara ta biyo bayan doguwar tattaunawar sulhu da 'yan bindigar domin kawo zaman lafiya a garuruwan jihar
  • Rahotanni sun bayyana cewa karamar hukumar Wase a jihar ta kasance mafi fuskantar hare-haren 'yan bindiga a jihar ta Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Filato - Wasu 'yan bindiga da suka addabi garuruwan karamar hukumar Wase a jihar Filato sun yada makamansu tare da miƙa wuya.

Gwamnatin Filato ta yi zaman tattaunawa da 'yan bindiga
'Yan bindiga sun mika wuya ga gwamnatin jihar Filato. Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Twitter

Gwamnatin jihar Filato ta sanar da hakan a ranar Litinin inda ta ce 'yan bindigar masu yawa sun mika bindigogi kirar AK47 ga gwamnati, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kungiyar fafutukar kafa kasar Yarabawa ta ba shugaba Tinubu wa'adin ware su daga Najeriya

Mai ba Gwamna Caleb Mutfwang shawara kan harkokin tsaro, kuma kwamandan rundunar Operation Rainbow, Birgediya Janar Gakji Shippi ya bayyana hakan a Jos.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Filato ta tattauna da 'yan bindiga

Janar Gakji Shippi ya bayyana cewa 'yan bindigar sun mika wuya tare da ajiye makaman su ne bayan doguwar tattaunawa tsakanin su da gwamnati.

Ya ce baya ga bindiga kirar AK47, akwai kuma sauran makamai da 'yan bindigar suka ajiye wanda ya nuna sadaukarwarsu ga zaman lafiya.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa akalla 'yan bindiga bakwai ne suka ajiye makaman nasu ta hannun wani da ya shiga tsakani yayin tattaunawar.

"Ku mika wuya" - Gwamnati ga 'yan bindiga

"Tare da bindigogin da 'yan bindigar suka ajiye akwai kuma sauran makamai da suka ajiye wadanda aka lalata su gaba daya."

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun halaka sojoji da dama a wani mummunan kwanton bauna

- Birgediya Janar Shipp.

Mai ba gwamna shawarar ya yi kira ga sauran 'yan bindiga a jihar da su mika wuya tare da ajiye makamansu.

Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar ta dauki matakai na ƙwato makamai daga kungiyoyin 'yan ta'adda domin daƙile hare-hare a karamar hukumar Wase.

'Yan binidiga sun sace mutane a Abuja

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa wasu 'yan bindiga sun kai sabon hari garin Dutse da ke babban birnin tarayya Abuja, inda suka yi awon gaba da mutane biyar.

A yayin wannan harin, an ce 'yan ta'addan su lakadawa wata mata dukan tsiya tare da kuma hadawa da yaranta biyu a cikin wadanda suka tafi da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel