Lamunin Karatu: Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Ya Nemawa Dalibai Alfarma Wajen Tinubu

Lamunin Karatu: Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Ya Nemawa Dalibai Alfarma Wajen Tinubu

  • Cif Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasar Najeriya ya ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan tsarin ba da lamunin dalibai
  • Obasanjo ya shawarci shugaban kasar da ya haɗa da daliban Jami'o'i masu zaman kansu domin samun abin da ake nema
  • Tsohon shugaban Najeriyan ya bayyana tsarin da wani mataki da zai kawo ci gaba da kuma walwalar jama'a a kasar baki daya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ogun - Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya ba Shigaba Bola Tinubu shawara kan lamunin dalibai.

Olusegun Obasanjo ya bukaci a sanya daliban jami'o'i masu zaman kansu a tsarin domin tallafa musu.

Tsohon shugaban kasa ya shawarci Tinubu kan lamunin ɗalibai
Olusegun Obasanjo ya ba Bola Tinubu shawara kan tsarin lamunin ɗalibai. Hoto: Bola Tinubu, Olusegun Obasanjo.
Asali: UGC

Tsoron Obasanjo kan lamunin karatu

Kara karanta wannan

"Allah kaɗai ke ba da mulki," Atiku ya mayar da martani kan zargin cin amana a taron NEC

Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne yayin wani taro a Jami'a Bells da ke Ota a jihar Ogun a jiya Litinin 22 ga watan Afrilu, a cewar rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obasanjo ya ce ya na tsoron yadda wannan lamari na bashin dalibai zai samu nasara ba tare da cin hanci ba, cewar Daily Post.

"Kamar yadda shugaban jami'ar ya fada kan sanya daliban Jami'o'i masu zaman kansu, ina kira da gwamnati da ta saurari wannan shawara."
"Tabbas yin hakan abu ne mai kyau sai dai ina tsoron cin hanci da rashawa a wannan lamari, wannan shi ne babbar matsalar."

- Olusegun Obasanjo

Obasanjo ya yabawa tsarin lamunin karatu

Tsohon shugaban kasar ya ce tabbas wannan tsari zai taimaka matuka wurin ci gaban Najeriya da kuma walwalar 'yan kasar.

Sai dai ya ce cire wani bangare ko kuma wani sashi na mutane zai kawo cikas wurin tabbatar da tsarin ya samu karɓuwa.

Kara karanta wannan

Mulkin Tinubu ya dara shekaru 16 a PDP ta fuskar tsaro, Hadimin Tinubu

Obasanjo ya shawarci Tinubu kan tattalin arziki

A baya, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya ba da shawara kan dakile matsalolin tattalin arzikin Najeriya.

Obasanjo ya ce idan har Shugaba Tinubu ya gaza shawo kan matsalar zai iya tuntubar kasar Zimbabwe domin neman taimakonsu.

Wannan na zuwa ne yayin da 'yan Najeriya ke cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa musamman kayan masarufi da ya addabi mutane a kasar..

Asali: Legit.ng

Online view pixel