Dangote Ya Sake Zabtare Farashin Dizal da Man Jiragen Sama, Ya Kafa Sharadi a Kasuwa

Dangote Ya Sake Zabtare Farashin Dizal da Man Jiragen Sama, Ya Kafa Sharadi a Kasuwa

  • Matatar mai ta Dangote ta sanar da kara rage farashin man dizal da na jiragen sama zuwa N940 da N980 a kan kowacce lita
  • Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake murnar matatar ta rage farashin dizal zuwa N1,000 a makonni biyu da suka wuce
  • Shugaban sashen sadarwa na rukunin Dangote, Anthony Chiejina ya ce za a sayi man a wannan farashin a gidajen mai na MRS

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A karo na biyu, matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin man dizal da na jiragen sama zuwa N940 da N980 kowacce lita.

Matatar man Dangote ka kara karya farashin dizal da man jiragen sama
Matatar man Dagote ta rage farashin dizal daga N1,000 zuwa N940. Hoto: Dangote Group (X) / Getty Images
Asali: Getty Images

Dangote ya karya farashin dizal

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake murnar matatar ta rage farashin dizal zuwa N1,000 a makonni biyu da suka wuce, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Farin ciki a jihar Arewa yayin da farashin shinkafa ya karye daga N60, 000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban sashen sadarwa na rukunin Dangote, Anthony Chiejina, wanda ya tabbatar da wannan sabon farashin a makon nan.

Anthony Chiejina ya ce matakin na daga kokarin da suke yi na rage wahalhalun tattalin arziki a Najeriya.

Chiejina ya bayyana cewa sabon farashin N940 ya shafi abokan cinikin da ke siyan lita miliyan biyar zuwa sama.

An tsaida farashin N970 ga masu sayen lita miliyan daya zuwa sama a hannun kamfanin na Dangote.

Dangote ya kulla yarjejeniya da MRS

"Matatar man Dangote ta kulla yarjejeniya da gidajen mai da mai na MRS domin tabbatar da cewa masu mutane sun sayi mai a farashi mai sauki.
"Kuna iya siyan dizal na ƙasa da lita 1 akan N1,050 da kuma man jiragen sama akan N980 a dukkan manyan filayen jiragen sama inda MRS ke aiki.”

Kara karanta wannan

Dizal zai iya karyewa zuwa N700/L, dillalan mai sun yabawa Dangote kan karya farashi

- Anthony Chiejina.

Jaridar The Punch ta rahoto shi yana cewa matatar za ta fadada irin wannan hadin gwiwar ga sauran manyan ‘yan kasuwar man nan ba da jimawa ba.

"Dizal zai iya komawa N700" - Dillalai

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa kungiyar dillalan mai ta Najeriya IPMAN ta ce akwai yiwuwar farashin Dizal zai kara karyewa har zuwa N700 kan kowase lita.

IPMAN ta bayyana hakan ne a lokacin da take tsokaci kan matakin matatar mai ta Dangode na karya farashin dizal wanda a cewarta hakan zai taimaka wajen kawo sauki a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel