Lauyoyi Sun Yi Zanga Zangar Rashin Yadda da Kama Yahaya Bello a Kotun Koli

Lauyoyi Sun Yi Zanga Zangar Rashin Yadda da Kama Yahaya Bello a Kotun Koli

  • Kungiyar lauyoyi ta Lawyers of Conscience ta yi zanga zanga a kotun koli domin nuna rashin goyon bayan kama Yahaya Bello da EFCC ke shirin yi
  • Shugaban kungiyar S.K Aremu ya ce yunkurin na hukumar EFCC abin Allah wadai ne lura da cewa ba ta bi umarnin kotu ba
  • Sannan kungiyar ta yi kira ga kungiyar lauyoyi da shugaban kasa domin su sa baki cikin lamarin domin kare martabar kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

A jiya Litinin ne lauyoyi su ka yi kawanya wa kotun Koli da ke birnin tarayyar Abuja domin nuna rashin goyon baya ga shirin kama tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

Kara karanta wannan

Hukumar FCCPC ta rufe kantin da ya hana 'yan Najeriya sayayya a Abuja

Hukumar EFCC tana zargin tsohon gwamnan ne bisa sama da fadi da dukiyar jihar Kogi a lokacin da yake gwamna.

Yahaya Bello
Kungiyar Lawyers of Conscience ta yi zanga zanga a kan kama Yahaya Bello a Abuja Hoto: Yahaya Bello
Asali: Facebook

A cewar jaridar Leadership, hakan na zuwa ne bayan da hukumar EFCC ta ɗaukaka kara a kan hana ta kama Yahaya Bello da wata kotu ta yi a Kogi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma hukumar ta EFCC ta ɗaukaka kara zuwa kotun koli kuma kotun ta saka ranar Litinin da ta wuce a matsayin ranar sauraron karar.

Sai dai kuma a jiya din magatakardan kotin kolin ya sanar da 'yan jarida cewa ba a saka karan cikin wadanda kotun za ta saurara ba.

Biyo bayan haka ne lauyoyin suka kutsa cikin kotun kolin suna zanga zangar cewa hukumar EFCC ba su da hurumin gurfanar da Yahaya Bello.

Yahaya Bello: Kungiyar lauyoyi ta koka

Kara karanta wannan

Kungiyar fafutukar kafa kasar Yarabawa ta ba shugaba Tinubu wa'adin ware su daga Najeriya

Lauyoyin da suke karkashin kungiyar Lawyers of Conscience sun ce kokarin EFCC na kama tsohon gwamnan duk da cewa kotu ta hana abin Allah wadai ne, cewar jaridar Vanguard

Shugaban kungiyar S.K Aremu ya ce babbar damuwarsu ba wai kama Yahaya Bello bane, yadda EFCC ta ke kokarin yi wa umarnin kotu karan tsaye ne babbar damuwarsu.

An yi kira ga Tinubu kan Yahaya Bello

Saboda haka kungiyar ta yi kira ga kungiyar lauyoyi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a kan su yi wa EFCC gargadi.

Kungiyar ta ce kokarin cin mutuncin kotu da EFCC ta ke yi a kan Yahaya Bello abu ne mai matukar muni kuma za ta cigaba da kokari wurin tabbatar da adalci da kare mutuncin kotu.

Magajin Yahaya Bello ya nemi taimako

A wani rahoton kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kogi ya nemi agajin gwamnatin Tarayya domin dakile matsalolin jihar da suka addabesu

Gwamna Usman Ododo ya bukaci taimakon ne inda ya ce jihar na neman mafita a ɓangaren rashin tsaro da kuma ambaliyar ruwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel