Rundunar Najeriya Ta Kori Sojojin da Aka Samu da Sata a Matatar Dangote

Rundunar Najeriya Ta Kori Sojojin da Aka Samu da Sata a Matatar Dangote

  • Hukumar sojin Najeriya ta sanar da korar sojoji biyu da ta kama da laifin sata a sabon matatar man Dangote a jihar Legas
  • Rundunar ta ce hukuncin ya biyo bayan zurfafa bincike ne a kan wadanda ake zargin da kuma ba su damar kare kansu
  • Ta kuma bayyana matakai da za ta cigaba da dauka da kuma yin kira mai muhimmanci ga daukacin al'ummar Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum

Jihar Lagos - Rundunar sojin Najeriya ta sanar da dakatar da sojojin da ta samu da laifin sata a matatar man Dangote da ke Legas.

Nigerian Army
Rundunar sojoji ta kori jami'ai saboda sata a matatar Dangote Hoto: HQ Nigerian Army/Dangote Refinery
Asali: Facebook

Menene dalilin dakatar da sojojin?

Rundunar ta dakatar da sojojin ne, Kofur Innocent Joseph da Lance Kofur Jacob Gani, bayan bincike da ta yi kuma ta tabbatar da cewa sun aikata laifin da ake zarginsu da shi.

Kara karanta wannan

Hukumar FCCPC ta rufe kantin da ya hana 'yan Najeriya sayayya a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba a manta ba dai a ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilu ne aka kama sojojin tare da zargi aikata laifin.

A yau Litinin, 22 ga watan Afrilu rundunar sojin ta fitar da sanarwar a shafinta na Facebook cewa an same su da laifi kuma an dakatar da su.

A cewar rundunar, an musu hukunci ne a bisa dokar aikin soja, kuma an ba su dama su kare kansu daga laifin amma sun gaza.

Me zai faru bayan dakatar da sojojin?

Rundunar ta tabbatar da cewa bayan dakatar da su an mika su ga hukumomin da suka dace domin ladabtarwa.

Hukumar ta ce wannan matakin da ta dauka ya nuna cewa ba za ta yarda da yin sakaci da zamba wurin gabatar da aiki ba.

Ta kuma yi kira ga daukacin al'ummar Najeriya da su ci gaba da goyon bayan ayyukanta domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a fadin ƙasar.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano gidan burodin 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda

A wani rahoton kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar rage mugun iri na ƴan ta'addan da suke aikata ayyukan ta'addanci a ƙasar nan

A yayin artabun da suka yi a jihohin Filato, Zamfara da Imo, jami'an tsaron sun sheƙe ƴan ta'adda biyu da ceto mutane mutane da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel