Kano da Jihohin da Ke Siyan Gas da Tsada, Akwai Sauki a Katsina Bayan Farashi Ya Tashi

Kano da Jihohin da Ke Siyan Gas da Tsada, Akwai Sauki a Katsina Bayan Farashi Ya Tashi

FCT, Abuja - Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta bayyana cewa a watan Maris an siyar da gas mai girman 5kg kan kudi N6,591 bayan tashin farashin.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Wannan karin shi yake nuna an samu karin kaso 7.1% idan aka kwatanta da watan Faburairu da ake siyarwa N6,154.

Jihohin da ke siyan gas da tsada da masu siya da araha
Kano na daga cikin jihohin da ke siyan gas da tsada yayin da farashin ya tashi. Hoto: Nurphoto.
Asali: Getty Images

Karin da aka samu kan farashin gas

Yayin da a cikin shekara farashin gas ya karu da kaso 42.9% idan aka kwatanta da N4,610 a watan Maris na shekarar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana amfani da wannan gas ne wajen yin girki da wasu aikace-aikace a gidaje.

Kara karanta wannan

Yayin da CBN ke kokarin kawo gyara, naira ta samu matsala a karo na 2, dala ta tashi

Jihohin da ke sayan gas da tsada (5kg)

1. Kano: N7,609.00

2. Ogun: N7,363.64

3. Akwa Ibom: N7,162.50

Jihohin da ke sayan gas da sauki (5kg)

1. Adamawa: N5,312.50

2.Taraba: N5,375.00

3. Zamfara: N5,550.00

Gas: Nawa ake sayen tulun kilo 12?

Har ila yau, NBS ta ce 'yan Najeriya na biyan N15,929 kan gas mai girman 12kg a watan Maris da ta gabata.

Hakan ya nuna an samu karin kaso 5.7 idan aka kwatanta da watan Faburairu kan N15,060, cewar The Guardian.

Yayin da a cikin shekara farashin ya karu da kaso 55.2% idan aka kwatanta da farkon shekarar bara.

A watan Maris na shekarar 2023 ana siyar da gas mai girman 12kg kan kudi N10, 262 idan aka kwatanta da watan Maris na wannan shekarar da aka siyar kan N15,929, cewar rahoton ThisDay.

Jihohin da ke siyan gas da tsada (12kg)

Kara karanta wannan

Jerin manyan jihohi 10 da farashin litar man fetur ya fi arha a Najeriya

1. Sokoto: N17,833.33

2. Osun: N17,588.46

3. Anambra: N17,417.65

Jihohin da ke siyan gas da sauki (12.5kg)

1. Katsina: N12,400.00

2. Kebbi: N13,137.50

3. Bauchi: N14,484.25

Wannan karin farashin gas na zuwa ne yayin da 'yan kasar ke kokawa kan tsadar man fetur da kayan masarufi.

Tashin farashin gas zai yi matukar tasiri ga rayuwar mafi yawan 'yan kasar ganin yadda suka dogara da shi domin yin abinci da sauran abubuwa na yau da kullum.

Tattaunawar Legit Hausa da wasu a Gombe

Legit Hausa ta tattauna da wasu masu siyar da gas a Gombe inda suka bayyana yadda farashin ya ke a wurinsu.

Muhammad Abubakar da ke siyar sa gas a Dubai Quarters a Gombe ya ce suna siyar da gas mai girman 3kg kan N4,200 sai 5kg kan N7,000.

Ya ce farashin 6kg ya kai N8,400 sai 12kg kuma suna siyarwa N16,800 har zuwa sama yadda mutum ke buƙata.

Kara karanta wannan

Farin ciki a jihar Arewa yayin da farashin shinkafa ya karye daga N60, 000

Har ila yau wani mai siyar da gas mai suna Musa Muhammad Ahmed shi ma ya ce suna siyar da kowane 1kg kan kudi N1,400 ne kacal.

Musa wanda shi ma ke Gombe ya ce lokacin azumi farashin ya tashi amma daga baya ya sake sauka, a hakan ma an samu ragi ne.

Dangote ya rage farashin litar dizal

A baya rahoto ya zo cewa kamfanin Aliko Dangote ya rage farashin litar dizal ga 'yan Najeriya domin samun sauki.

Matatar ta rage farashin ne daga 1,200 zuwa N1,000 yayin da 'yan kasar ke cikin mawuyacin halin matsin rayuwa.

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yabawa Aliko Dangote kan wannan mataki inda ya ce hakan zai kawo raguwar farashin kayayyaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel