Abba Gida Gida ya Nada Tauraro Abba El-Mustapha da Wasu Mutane 14 a Gwamnati

Abba Gida Gida ya Nada Tauraro Abba El-Mustapha da Wasu Mutane 14 a Gwamnati

  • Abba Kabir Yusuf ya nada shugabannin wasu hukumomi, cibiyoyi da kamfanonin jihar Kano
  • Mai girma Gwamnan ya ba Dr. Muhammad Khalil da Dr. Dahir Hashim matsayi a (KN-WECCMA)
  • Hukumomin gwamnati na KASCO, KHEDCO, KSIP da KNARDA sun yi sababbin shugabanni

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Mai girma Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin wasu mukami a jihar Kano kamar yadda wata sanarwa ta fito a safiyar Larabar nan.

Sanusi Bature Dawakin Tofa wanda shi ne babban Sakataren yada labarai na Gwamnan Kano ya fitar da jawabi a shafinsa na Facebook dazu.

Abba Gida Gida ya nada sababbin shugabannin hukumomin gwamnati da su ka hada da RUWASA, KASCO da kuma hukumar tace fina-finai.

Abba Gida Gida
Gwamnatin Jihar Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Daga cikin wadanda aka ba mukaman akwai Sani Bala, Dahir M. Hashim da Tukur Bala Sagagi

Kara karanta wannan

Masu ba Gwamnan Kano Shawara Sun Doshi 50 Bayan Nade-Naden Sababbin Mukamai

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jerin mukaman da aka bada

1. Injiniya Ado Ibrahim Umar, Shugaban kamfanin wutar lantarki (KHEDCO).

2. Alhaji Auwalu Mukhtar Bichi, Shugaban kamfanin jawo hannun jari (KSIP).

3. Dr. Farouq Kurawa, Shugaban hukumar kula da aikin gona da raya karkara (KNARDA)

4. Dr. Tukur Dayyabu Minjibir, Shugaban hukumar samar da kayan gona (KASCO)

5. Hon. Hussain Sarki Aliyu Madobi, Shugaban aikin SKP

6. Hon. Sadiq Kura Muhammad, Shugaban gidan dabbobi (ZGK)

7. Injiniya Sani Bala, Shugaban hukumar kula da wutar lantarki a karkara (REB)

8. Hon. Shamwilu Gezawa, Shugaban hukumar ruwa (RUWASA)

9. Alh. Tukur Bala Sagagi, Shugaban hukumar yawon bude ido

10. Alh. Yahaya Muhammad, Shugaban kamfanin madaba’ar Kano.

11. Hon. Adamu Yahaya, Mataimakin shugaban kamfanin madaba’ar Kano.

12. Abba El-mustapha, Shugaban hukumar tace fina-finai.

13. Dr. Muhammad S. Khalil, Shugaban hukumar kula da zaizayewar kasa da sauyin yanayi (KN-WECCMA)

14. Dr. Dahir M. Hashim, Mai kula da hukumar kula da zaizayewar kasa da sauyin yanayi (KN-WECCMA)

Kara karanta wannan

Kura-Kurai, Katobara da Cikas 7 da Abdullahi Adamu Ya Samu a Kujerar Shugabancin APC

Babu mace ko daya cikin mukamai 14

Legit.ng Hausa ta lura a cikin mukaman da aka raba, babu mace ko daya. Baya ga haka matasa su na kukan cewa ya kamata a rika yi da su.

Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bada umarni ga wadanda aka zaba da su fara aiki gadan-gadan a ofisoshinsu.

Nade-naden mukaman Abba

A cikin makon nan ne dai aka ji labari Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada Mai bada shawara a kan sha’anin ciniki da wasu Hadimai fiye da goma.

Rt. Hon. Isyaku Ali Danja zai rika ba Gwamnatin Kano shawara a kan harkokin majalisar dokoki, Sheikh Usamatu Salga ya samu matsayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng