Ba’a Kyauta Mana Mu Talakawa: Rukayya Dawayya ta Koka Kan Yadda ‘Ya’yan Masu Kudi Ke Auran Junansu A Kasar

Ba’a Kyauta Mana Mu Talakawa: Rukayya Dawayya ta Koka Kan Yadda ‘Ya’yan Masu Kudi Ke Auran Junansu A Kasar

  • Jarumar Kannywood, Rukayya Dawayya ta shawarci 'ya'yan talakawa da su farka daga baccin da suke yi domin 'ya'yan masu kudin da ke soyayya da su ba aurensu za su yi ba
  • Dawayya ta ce sam masu kudi basa yiwa talakawa adalci domin basa yarda 'ya'yansu su auri kowa sai 'ya'yan masu kudi yan uwansu
  • A cikin bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya, jarumar ta kalubalanci ‘ya’yan talakawa da su tashi su nemi ilimi don kare mutuncin kansu a kasar nan

Najeriya - Shahararriyar jarumar Kannywood, Rukayya Umar Dawayya ta yi martani a kan yadda ake yin kwarya tabi kwarya wajen kulla auratayya a kasar nan.

Dawayya ta shawarci ‘ya’yan talakawa da ke da kyau a kan su daina yarda da soyayya tsakaninsu da yaran masu kudi domin magana ta gaskiya ba auransu za su yi ba.

Kara karanta wannan

Shin tana kanne: Martanin 'yan Najeriya ga bidiyon wani matashin da ya yi wuff da baturiya

A cewarta koda yaran na son su iyayensu ba za su amince a kawo masu diyar talakawa a matsayin suruka ba, don haka ta shawarce su da su tashi su nemi ilimi don gobensu.

Rukayya Dawayya
Ba’a Kyauta Mana Mu Talakawa: Rukayya Dawayya ta Koka Kan Yadda ‘Ya’yan Masu Kudi Ke Auran Junansu A Kasar Hoto: @dawayyarukayya85
Asali: Instagram

Jarumar fim din tayi misali da abun da ke faruwa a kasar yanzu haka inda tace duk auren da ake yi a yanzu tsakanin ‘yar wane da dan wane ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta ce sai ka ga namiji kamar shi yayi kansa da kyau amma matarsa kamar a yanka a boye wuka don muni amma ya yarda ya aureta saboda ita din yar wani ce.

A cikin bidiyonta da ya yadu a soshiyal midiya, an kuma jiyo jarumar tana kokawa kan cewa ba a yiwa talaka adalci a kasar nan domin kamata yayi a dunga bari dan mai kudi ya auri yar talaka, yar mai kudi ta auri dan talaka.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Ya kamata daliban jami'a su maka ASUU a kotu, su nemi diyyar bata lokaci

A cewarta ta haka ne za a samu arzikin ya kai gidan kowa amma masu kudin sam basa kaunar ganin haka.

Don haka ta shawarci ‘ya’yan mallam shehu wato talakawa da su dage da neman ilimin addini tunda har na Bokon ana so a hana su yi sakamakon yajin aikin da ake zuwa.

Wani bangare na jawabin nata na cewa:

“Wani abu ne yake damuna kullun idan na ga abun nan sai ya tsayamun a raina. Kun ga yaran nan zuwa nayi na baku shawara, ‘ya’yan mallam Shehu yan uwana, ‘ya’yan talakawa billahillazi ku kama kanku, kun ga kuna da kyau kuna da wayewa, ‘ya’yan masu kudi da suke zuwa suke karya suna soyayya da ku wallahi amfani suke yi da kyau da kuruciyarku babu dan mai kudin da zai iya zuwa gidan babansa ya kai sunanki wai zai aure ki.
“Wai dan Allah baku lura da abun da ke faruwa bane yasu-yasu suke haduwa suke aure, jama’a wannan wani irin rashin kara ne kuke mana masu kudin kasar nan? Da me za a ji ai sai ana aurataitaniya a tsakani sannan za a samu arziki ya shiga gidan kowa. Yar talaka ta auri dan mai kudi, yar mai kudi ta auri dan talaka duk wanda ya ga wanda yake so a bashi amma sai ki ga ango zukeke kamar shi yayi kansa matarsa kamar a yanka a boye wuka don muni amma ya aureta saboda yar wani ce.”

Kara karanta wannan

Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Yayin da Ta Iso Najeriya Don Haduwa Da Saurayinta Na Soshiyal Midiya

Kalli cikakken bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

usamatu_auwal ya ce:

"Wallahi wannan gaskiyane."

kays_notch ta ce:

"Kwarya tabi kwarya dan Allah ."

raihannabrahamxx ta ce:

"Wayyyooo."

reall_me_and_i ya ce:

"Kaji er tsurku in kwarya taci gaba da bin kwarya ai talauci zai cika duniya."

thelacesemporium ta ce:

"Wannan magana gaskiya ce... Kwarya tabi kwarya kawai akeyi."

ummkaleelwakaleem ta ce:

"Maganar ki dutse... A Inda su ka fi bukatan talakawa shine wurin Yan aikin gida, Yan aike, da wurin Yi masu bangar siyasa... Allah ya sa mu Gane, mu mutunta kan mu."

Burina Na Zama Babbar Attajira Sunana Ya Danne Na Dangote – Maimuna Wata Yarinya

A wani labarin, Shahararriyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Maimuna Muhammad wacce aka fi sani da ‘Wata Yarinya’ ta bayyana babban burinta a rayuwa.

A cewar matashiyar jarumar wacce take haifaffiyar yar Maiduguri burinta shine ta zama babbar attajira kuma yar kasuwa.

Kara karanta wannan

Har Yanzu Sabo Fil Nake: Bidiyon Tsoho Dan Shekaru 90 Wanda Bai Taba Yin Budurwa Ko Mata Ba

Ta ce za ta so duaceniya ta santa a wannan fage na kasuwanci ta yadda zai kai sunanta ya danne na mai kudin Afrika kuma shahararren dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote.

Asali: Legit.ng

Online view pixel