Baturiya Ta Yi Wuff da Matashi Dan Najeriya, Jama’a Sun Yi Cece-Kuce a Intanet

Baturiya Ta Yi Wuff da Matashi Dan Najeriya, Jama’a Sun Yi Cece-Kuce a Intanet

  • Matashi dan Najeriya da ya jawo ma kansa magana yayin da auri wata budurwa farar fata kuma ya yada bidiyonsu a intanet
  • Wani mutumin da ya fusata da yadda 'yan matan turai ke kwashe samari 'yan Najeriya ya sha martani mai zafi cikin sauki
  • Jama'ar soshiyal midiya dai ba abin da suke sai yaba masa da samun galleliyar budurwa mai hasken fata, wasu kuwa na fatan samun irin wannan banza su kwasa

Matashi dan Najeriya da ya gwangwaje wajen zabo mata, ya auro wata baturiya, inda ya yada bidiyonsu mai ban sha'awa, amma ya jawo cece-kuce a intanet.

Wani ya yi martani bayan ganin bidiyon, lamarin ya kai ga angon ya fadi wata maganar da ta tada kura.

A faifan bidiyon, an ga baturiyar da matashin sanye da zoban amarcewa da na angwancewa yayin da suke bankwana da Najeriya acikin jirginsa sama.

Kara karanta wannan

Kamar almara: Sauyawar wani matashi daga sana'ar acaba zuwa tauraro ya ba da mamaki

Yadda batuiya ta yi wuff da matashi dan Najeriya ya jawo cece-kuce
Baturiya Ta Yi Wuff da Matashi Dan Najeriya, Jama’a Sun Yi Cece-Kuce a Intanet | Hoto: TikTok/@bullaumeh
Asali: UGC

Amsar da ya ba wani mutumin da ya nemi gaya masa magana mara dadi ta burge jama'a, kuma dan 'yan Najeriya da dama sun ce su ma din dama kawai suke jira a yi wuff dasu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa, ita soyayya ba ta da madakata, kuma ba ruwanta da hasken fata da duhunsa.

Wasu kam ma cewa suke, idan amaryar tasa na da 'yan uwa to don Allah a hada su domin samun irin wannan aure na fara fata.

Kalli bidiyon:

Martanin 'yan TikTok

Bidiyon dai ya samu karbuwar jama'a, kuma mutane sama da 200 ne suka tofa albarkacin bakinsu. Ga kadan daga ciki:

@@usiego ya ce:

"...''Yan matanmu na nan sai cinye mana kudi suke, kuma gashi ba sa taimakonmu."

@4pf142 ya ce:

"Ni dai fara fata zan aura, idan har abokiyar rayuwa na nan Naija Allah yasa na tabbata tuzuru."

Kara karanta wannan

Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Yayin da Ta Iso Najeriya Don Haduwa Da Saurayinta Na Soshiyal Midiya

@Gabriel yace:

"Ya ne kam, ba ta da 'yar uwa kanwa ne da za a hada ni da ita na aura."

@Mylx yace:

"Gashi mu kuma 'yan uwanmu ba su da hankali."

@Kim_Chris_jellum yace::

"Yayin da 'yan uwanmu mata a nan suka mai da hankali kan karuwanci, me kuke so mu aura."

@476truth yace:

"Ga 'yan uwanka a nan ba sa jin magana."

@ChettyFdont> yace:

"Hahahaha ka yi abinda kake so, ka yi shanawarka."

Yadda Wani Dan Acaba Ya Gamu da Mutumin Kirki, Ya Sauya Shi Zuwa ‘Celebrity'

A wani labarin, wani dan TikTok mai suna @alber_noir, ya yada wani gajeren bidiyo na yadda rayuwar wani dan acaba ta sauya daga cakwalkwali zuwa nasara.

Tun farin faifan bidiyon da aka yada a TikTok, mutumin ya bayyana cewa, shi dai abin da kawai yake dashi a rayuwa ba komai bane face fatan nasara.

A wani sashe na bidiyon kuwa, ya nuna shi fa a baya dan acaba ne, don haka ga ma babur din da yake tare kebura da ita.

Kara karanta wannan

Namijin Kirki Ba Zai Yi Soyayya Da Budurwa Fiye Da Shekara Ba Tare Da Ya Aure Ta Ba – Hadimin Gwamna

Asali: Legit.ng

Online view pixel