Ya Zama Dole ASUU Ta Biya Diyya Ga Daliban da Suka Batawa Lokaci, inji Minista Adamu

Ya Zama Dole ASUU Ta Biya Diyya Ga Daliban da Suka Batawa Lokaci, inji Minista Adamu

  • Yayin da ake ta tunanin yadda za a shawo kan matsalar ilimi a Najeriya, ganin yadda ASUU ke yaji, ministan ilimi ya kawo wani batu
  • Adamu Adamu ya yi kira ga dalibai da su gaggauta maka ASUU a kotu tare da neman diyyar lokacin da aka bata musu
  • Akalla watanni shida aka bata a Najeriya dukkan jami'o'i na garkame saboda yajin aikin da malamai ke yi

FCT, Abuja - Ministan Ilimi a Najeriya, Adamu Adamu, a ranar Alhamis, ya ce alhakin kungiyar malaman jami’o’i ne ta biya daliban jami'a diyyar lokacin da suka bata yayin yajin aikin na watanni shida na ASUU ba gwamnatin tarayya ba.

Ya kuma ce gwamnati ba za ta amince da bukatar kungiyar na biyan malamai kudaden alawus-alawus din su na tsawon watanni shida da suka bata ba tare da aikin karantarwa ba, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ba Za a Bude Jami’o’i Kwanan nan ba, ASUU Tayi Magana Kan Dogon Yajin-Aikinta

Ya kamata daliban Najeriya su maka ASUU a kotu, inji Adamu Adamu
Ya zama dole ASUU ta biya diyya ga daliban da suka bata – Minista | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Adamu ya ba da shawarar cewa daliban da abin ya shafa su kai ASUU kotu domin neman diyya bisa lokacin da kungiyar ta bata musu yayin yajin aikin.

Ministan Ilimin ya bayyana haka ne a wajen zama na 47 na taron manema labarai na Majalisar Dokokin Kasa da tawagar Shugaban kasa kan sadarwa ta shirya a fadar Aso Rock Villa, Abuja.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa, gwamnatin tarayya ba ta da wani dalili ko alhakin biyan miliyoyin daliban da aka sanya a tasku na tsawon watanni shida saboda da sunan yaji, rahoton Daily Trust.

Ya kuma ce idan daliban sun kuduri aniyar neman diyya to su gurfanar da ASUU a kotu.

Kada Ku Zabi Dan Siyasar Da ’Ya’yansa Ke Karatu a Waje, Inji Shugaban ASUU

A wani labarin, shugaban kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) Farfesa Emmanuel Osodeke, a ranar Laraba shawarci daliban Najeriya kada su zabi ‘yan siyasar da ‘ya’yansu ke karatu a makarantun kasashen waje, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ma'aikatan Lantarki A Najeriya Sun Dakatar Da Yajin Aiki Bayan Ministan Kwadago Ya Zauna Da Su

Osodeke ya yi magana ne a shafin Twitter Space Webinar, wanda Premium Times ta shirya mai taken,‘ASUU strike, Revitalisation Fund and the Way Forward’ don nemo mafita ga mafitan yajin ASUU.

Da yake magana kan wasu hanyoyin ci gaba na mafita ga yajin aikin, ya ce kada dalibai su zabi ‘yan siyasar da ba za su wakilci muradunsu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel