Har Yanzu Sabo Fil Nake: Bidiyon Tsoho Dan Shekaru 90 Wanda Bai Taba Yin Budurwa Ko Mata Ba

Har Yanzu Sabo Fil Nake: Bidiyon Tsoho Dan Shekaru 90 Wanda Bai Taba Yin Budurwa Ko Mata Ba

  • Baizire Jean Marie ya kasance dan shekaru 90 wanda bai taba yin soyayya ba, haka bai haifi ‘ya’ya a waje ba
  • Abun da ke ba mutane mamaki game da labarin mutumin shine cewa bai da wata matsala ta jiki ko kwakwalwa
  • Wasu mutane a garin Baizire wadanda ke mu’amala da shi suna hasashen akwai mutanen boye a kan lamarinsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani tsoho dan shekaru 90 mai suna Baizirre Jean Marie ya bayyana cewa har yanzu a kasuwa yake baida aure.

Kafar labarai ta Afrimax English ta ziyarci kauyen mutumin kuma sun zanta da shi, inda ya bayyana matsayinsa a soyayya.

Tsoho
Har Yanzu A Kasuwa Nake: Bidiyon Tsohon Dan Shekaru 90 Wanda Bai Taba Yin Budurwa Ko Mata Ba Hoto: YouTube/Afrimax English
Asali: UGC

Baizire ya bayyanawa kafar labaran cewa ya tsaya ne a aji biyar na makarantar firamare, wanda yace bai tsinana masa komai ba.

Ya bayyana cewa ya shafe tsawon rayuwarsa ne a kauyen kuma bai taba yin soyayya ko haihuwar da a waje ba.

Kara karanta wannan

Namijin Kirki Ba Zai Yi Soyayya Da Budurwa Fiye Da Shekara Ba Tare Da Ya Aure Ta Ba – Hadimin Gwamna

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ana kirana Baizire Jean Marie. Shekaruna 90 a duniya. Na shafe tsawon rayuwa ne a wannan kauyen kuma ban taba aure ba kuma ban taba tarayya da mace ba. Hakan na nufin, har yanzu ni saurayi ne.”

Baizire bai da wata nakasa ko matsalar kwakwalwa da zai sa mata gudunsa. Tsohon ya dogara ne da yan uwa ta bangaren abinci da sauran abubuwan rayuwa domin bashi da wani aikin yi.

Mutanen kauyensa da suka zanta da Afrimax sun ce suna zargin yana da matsala ta mutanen boye.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama’a

Lorie Logan ya ce:

“Allah ya albarkaci zuciyarsa saurayi dan shekaru 90. Ya yi kokari sosai da rashin tarayya da mace.”

Christine Achieng ta ce:

“Yana da karfi kuma har yanzu yana gwagwarmaya Allah ya bashi tsawon rai ya fi shekaru 100.”

Kara karanta wannan

Bidiyo: Sauyawar Wata Zukekiyar Budurwa Ya Haddasa Cece-Kuce A Yanar Gizo, Ta Kara Kyau Da Haduwa

julia herbet ta ce:

“Afrika mun yarda da maita da mutanen boye sosai..kawai dai watakila yana jin kunyar tunkarar mace ne.”

jumoke Aladese ta ce:

“Allah ya yi masa albarka ya fi shekarunsa kyau, babu aibu don mutum bai da mata, yana da soyayya da goyon baya sosai daga yan uwansa. Ina addu’an Allah yasa ya samu karin taimako.”

Hotunan Tsoho Mai Shekaru 62 Wanda Ya Yi Shekaru 22 Ba Wanka

A wani labarin, Dharamdev Ram, ya kasance tsoho mai shekaru 62 daga yankin Bihar a kasar Indiya kuma ya shafe tsawon shekaru 22 ba tare da ya yi wanka ba.

Al’ummar kasar Indiya sun yi martani bayan samun wannan labari na rashin wankan Ram, Aminya ta nakalto.

Ram dai ya yi suna sosai a kauyensa na Baikunthpur, inda kowa ya san cewa baya sanyawa kowani bangare na jikinsa ruwa tsawon shekaru 22.

Kara karanta wannan

Matashi Dan Shekaru 27 Zai Yi Wuff Da Budurwarsa Mai Shekaru 74 Wacce Ke Tuna Masa Da Kakarsa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng