Burina Na Zama Babbar Attajira Sunana Ya Danne Na Dangote – Maimuna Wata Yarinya

Burina Na Zama Babbar Attajira Sunana Ya Danne Na Dangote – Maimuna Wata Yarinya

  • Jarumar Kannywood, Maimuna Muhammad wacce aka fi sani da wata yarinya ta ce babban burinta a rayuwa shine ta zama attajirar yar kasuwa
  • Maimuna wata yarinya ta ce tana burin ganin ta shahara a fannin kasuwanci ta yadda sunanta zai danne na Dangote ya zama duniya ta san da ita
  • Jarumar ta kuma ce tana burin ganin ta yi aure ta samu zuri'a dayyiba tare da gamawa da duniya lafiya

Najeriya - Shahararriyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Maimuna Muhammad wacce aka fi sani da ‘Wata Yarinya’ ta bayyana babban burinta a rayuwa.

A cewar matashiyar jarumar wacce take haifaffiyar yar Maiduguri burinta shine ta zama babbar attajira kuma yar kasuwa.

Ta ce za ta so duaceniya ta santa a wannan fage na kasuwanci ta yadda zai kai sunanta ya danne na mai kudin Afrika kuma shahararren dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote.

Kara karanta wannan

Gaskiya Mijinki Ya Iya Kiwo: Hotunan Matar Aure Na Da da Yanzu Ya Haddasa Cece-kuce

Maimuna wata yarinya
Burina Na Zama Babbar Attajira Sunana Ya Danne Na Dangote – Maimuna Wata Yarinya Hoto: watayarinya
Asali: Instagram

Maimuna wata yarinya ta bayyana hakan ne a yayin wata da hira da tayi da sashin Hausa na BBC a shirin ‘Daga bakin mai ita’. An tambaye ta menene babban burinta a rayuwa nan gaba inda ta ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Ka san shi dan adam yana da buri a rayuwa. Burina shine a duniyarmu ta yanzu da muke cikinta Ubangiji Allah yasa mu gama da duniya lafiya, shine burin mutum na farko. Sannan kuma burin mutum ba zai wuce yayi aure ya samu zuri’a dayyiba ba a rayuwa, toh wannan ma ina da buri.
“Amman ni burina shine ina so na zama irin attajiran macen nan yar kasuwa. Wanda irin ace zan zo ma in danne Dangote a suna, sai ace Hajiya Maimuna wata yarinya. Ka ga kowa yana da burinsa amma ni ina so in zama attajirar yar kasuwa wanda duk duniya za ta san da ita."

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Amarya Ta cafke Dalolin Da Aka Lika Mata A Wajen Liyafar Bikinta

Bidiyoyin Cikin Dankareren Gidan Da Jaruma Sadiya Haruna Ta Ginawa Mahaifiyarta

A wani labari na daban, Jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood kuma mai daukar hankali a kafafen sada Zumunta ta Instagram, Sayyada Sadiya Haruna, ta gwangwaje mahaifiyarta.

Sadiya ta dankarawa mahaifiyar tata wani katafaren gida domin ta more tare da cin ribar haihuwarta da tayi.

Sau da dama jarumar ta sha fitowa tana bayyana irin soyayyar da take yiwa mahaifanta musamman ma mamar tata, sannan ta sha cewa a kullun cikin yi mata addu’a suke don haka ita ma take son farin cikinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel