Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Yayin da Ta Iso Najeriya Don Haduwa Da Saurayinta Na Soshiyal Midiya

Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Yayin da Ta Iso Najeriya Don Haduwa Da Saurayinta Na Soshiyal Midiya

  • Wasu masoya farar fata da bakin fata sun taba zukata a soshiyal midiya da soyayyarsu yayin da suka hadu ido da ido
  • Bayan shafe tsawon shekara daya suna soyayya a soshiyal midiya, kyakkyawar Baturiyar ta iso Najeriya don haduwa da saurayinta bakin fata
  • An dauki bidiyon haduwarsu ta farko sannan aka yada shi a soshiyal midiya kuma ya kayatar da mutane

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Wasu masoya bakin fata da Baturiya da suka kulla soyayya ta soshiyal midiya tsawon shekara daya sun hadu ido da ido.

Mutumin mai suna Chris Kizito ya kasance cike da farin ciki yayin da baturiyar budurwar tasa, Jessie ta iso Najeriya.

Saurayi da budurwa
Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Yayin da Ta Iso Najeriya Don Haduwa Da Saurayinta Na Soshiyal Midiya Hoto: TikTok/@chriskizito
Asali: UGC

A wani dan gajeren bidiyo a TikTok, an gano yadda Chris ya rungume ta bayan ya hango ta a filin jirgin sama, yayin da wani dan uwansa ya taimakawa Jessie wajen daukar kayanta.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Sauyawar Wata Zukekiyar Budurwa Ya Haddasa Cece-Kuce A Yanar Gizo, Ta Kara Kyau Da Haduwa

Masoyan sun sumbaci junansu kafin suka fito daga filin jirgin saman.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit.ng ta tattaro cewa ma’auratan sun shiga daga ciki. Shafin TikTok din mutumin @chriskizito yana ta wallafa kyawawan bidiyoyin masoyan na ban dariya.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

King Kounga ya ce:

"Waooooooo na taya ka murna dan uwana… Na san abun ba sauki ko kadan."

Koks_seh1 ta ce:

"Kalli yadda yake ta ririta ta. Da yar Najeriya ce ina tantama idan zai kula da ita haka.
"Ba da dadewa ba duniya za ta san cewa har yanzu akwai nagartattu a yan matan Najeriya."

Jay John ya ce:

"Na taya ka murna dan uwa. Duba shafina nima. Na yi matukar farin ciki lokacin da tawa ta zo nan."

Matashi Dan Shekaru 27 Zai Yi Wuff Da Budurwarsa Mai Shekaru 74 Wacce Ke Tuna Masa Da Kakarsa

Kara karanta wannan

Matashi Dan Shekaru 27 Zai Yi Wuff Da Budurwarsa Mai Shekaru 74 Wacce Ke Tuna Masa Da Kakarsa

A gefe guda, wasu masoya wadanda suka hadu a shafin soshiyal midiya sun bayyanawa duniya irin son da suke yiwa junansu.

Kathi Jenkins mai shekaru 74 ta hadu da Devaughn Aubrey mai shekaru 27 inda suka yi zurfi a soyayya kuma a yanzu haka, masoyan wadanda suka fito daga Texas sun yi baiko kuma za su shiga daga ciki.

Kasancewar sun shafe tsawon shekara fiye da daya a soyayya, Devaugh ya ce ya san tsohuwar mai shekaru 74 ita ce burin ransa, shafin LIB ya rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel