JD Vance: Mataimakin Trump Ya Fito da Ainihin Dalilan da Suka Jawo Rashin Nasararsu a Zabe

JD Vance: Mataimakin Trump Ya Fito da Ainihin Dalilan da Suka Jawo Rashin Nasararsu a Zabe

  • JD Vance ya ce yawancin magoya bayan Donald Trump da suka zaɓi tikitin Trump-Vance a 2024 sun koma zaɓen ’yan Democrat a 2026
  • Yaƙin Iran, tsadar rayuwa, hauhawar farashi da manufofin ƙasashen waje na Amurka na daga cikin dalilan da suka sa masu zaɓe suka juya wa Republican baya
  • Vance ya ce masu zaɓen da suka sauya sheƙa sun buƙaci a kawo ƙarshen yaƙin, a fifita Amurka da kuma sauya dangantakarta da Isra’ila

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, ya danganta rashin nasarar jam’iyyar Republican a zaɓen tsakiyar wa’adi na shekarar 2026 da yaƙin Iran.

Vance ya ce da dama daga cikin magoya bayan Shugaba Donald Trump sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar Democrat saboda rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da yaƙin.

JD Vance ya yi magana kan rashin nasarar jam'iyyarsu
JD Vance na gabatar da jawabi a wajen taro Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamban 2026 inda ya yi ƙarin haske kan dalilan da suka sa jam’iyyarsa ta fuskanci koma baya a zaɓen.

Kara karanta wannan

Yadda masu Opay za su iya karbar tallafin N50,000 duk wata na gwamnatin tarayya

A cewarsa, rashin fitowar masu zaɓe ba shi ne babban dalilin rashin nasarar ba, illa sauya sheƙar mutanen da suka zaɓi tikitin Trump da Vance a zaɓen 2024.

Vance ya ce ba batun ƙarancin masu zaɓe ba ne

Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa nazarin bayanan da tawagarsa ta gudanar kafin zaɓen ya nuna cewa magoya bayan Republican na shirin fitowa kada ƙuri’a sosai.

Ya ce hakan ya bambanta da hasashen wasu ƙuri’un jin ra’ayin jama’a da suka nuna cewa jam’iyyar Democrat za ta samu gagarumar nasara.

Vance ya ce ɗaya daga cikin abubuwan da masu nazarin bayanai na jam’iyyarsu suka mayar da hankali a kai shi ne yadda tsarin masu zaɓe zai kasance idan aka kwatanta da zaɓen 2024.

Ya bayyana cewa sun yi ƙoƙarin tantance ko yawan masu zaɓe da tsarin goyon bayansu zai yi kama da na 2024, wanda zai iya ba Republican damar yin nasara.

Sai dai ya ce wani ma’aikacin tawagarsa ta nazarin bayanai ya gargaɗe shi cewa da dama daga cikin magoya bayan jam’iyyar na cikin fushi, kuma akwai yiwuwar ba za su sake zaɓar ta ba.

Kara karanta wannan

Atiku ya kaddamar da kamfen a Sokoto, ya yi muhimman alkawura ga 'yan Najeriya

Vance ya ce abin da ma’aikacin ya yi hasashe ya bayyana a sakamakon zaɓen.

“Masu zaɓenmu sun fito. A Florida, alal misali, masu zaɓen Republican sun fi na Democrat da maki tara, wanda hakan ya yi ƙasa da na zaɓen 2024 da maki kaɗan kawai.

"Amma babbar matsalar ba ƙarancin masu zaɓe ba ce. Babbar matsalar ita ce mutane da dama da suka zaɓi Trump da Vance a 2024 sun zaɓi ’yan Democrat a 2026.” In ji shi.

Yaƙin Iran da tsadar rayuwa sun shafi zaɓen

Mataimakin shugaban ƙasar ya amince cewa wataƙila jam’iyyarsu ta gaza isar da manufofinta na tattalin arziki ga jama’a yadda ya kamata.

Musamman ma, ya ambaci matsalolin tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki a matsayin batutuwan da jam’iyyar ba ta yi wa jama’a cikakken bayani a kansu ba.

Sai dai Vance ya ce manyan dalilan da suka sa masu zaɓe suka juya wa Republican baya sun haɗa da damuwa kan yaƙin Iran, matsin tattalin arziki da yadda Amurka ke tsara manufofinta na ƙasashen waje.

Kara karanta wannan

Jerin 'yan Najeriya 4 da suka lashe kujeru daban daban a zaɓen Amurka, na 5 na hanya

Ya kuma ambaci dangantakar Amurka da Isra’ila a matsayin ɗaya daga cikin batutuwan da suka shafi ra’ayin masu zaɓe.

JD Vance ya yi magana kan zaben Amurka
JD Vance na jawabi a wajen taro Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Abubuwa 4 da masu zaɓe suka nema

A cewar Vance, wani mai gudanar da binciken ra’ayin jama’a wanda ya yi hasashen sakamakon zaɓen daidai, ya gano manyan buƙatu huɗu daga tsoffin magoya bayan Republican da suka sauya sheƙa zuwa Democrat.

Buƙatun sun haɗa da kawo ƙarshen yaƙin, mayar da hankali kan tsadar rayuwa da hauhawar farashi, fifita muradun Amurka da kuma sauya dangantakar ƙasar da Isra’ila.

Vance ya jaddada cewa yaƙin Iran ne ya fi tasiri wajen jawo wa jam’iyyarsu rashin nasara.

“Dalilin da ya sa muka sha kaye shi ne yaƙin. Shugaban ƙasar da kansa ya faɗi hakan a daren jiya.” In ji shi.

Trump ya yi magana kan yiwuwar tsige shi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Donald Trump ya yi martani kan yiwuwar jam'iyyar Democrat ta fara shirin tsige shi daga mulki bayan ta karɓe rinjaye a majalisun dokokin Amurka a zaɓen tsakiyar wa'adin mulki.

Trump ya bayyana cewa idan Democrat suka ɗauki matakin tsige shi bayan fara sabon zaman majalisa a watan Janairu, hakan zai iya jawo wa jam'iyyar babbar matsala a siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng