Obama Ya Ce za a Fara Shirin Rage 'Barnar' Trump bayan Kwace Ikon Majalisa

Obama Ya Ce za a Fara Shirin Rage 'Barnar' Trump bayan Kwace Ikon Majalisa

  • Tsohon Shugaban Amurka, Barack Obama, ya yi martani bayan jam'iyyarsa ta Democrat ta samu nasara a zaɓen tsakiyar wa'adin mulkin ƙasar
  • Obama ya ce sakamakon zaɓen ya nuna cewa Amurkawa na son shugabanci da ke haɗa kan jama'a maimakon rarrabasu
  • Ya kuma buƙaci 'yan jam'iyyarsa su mayar da hankali wajen kawo sauye-sauye da rage illolin manufofin gwamnatin Trump cikin shekaru biyu da suka rage mata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Tsohon shugaban ƙasar Amurka, Barack Obama, ya yi magana bayan jam'iyyarsa ta Democrat ta samu nasara a zaɓen tsakiyar wa'adin mulkin ƙasar, inda ya bayyana cewa sakamakon ya nuna irin shugabancin da al'ummar ƙasar ke buƙata.

Obama ya ce jama'ar Amurka sun aika da saƙo karara cewa suna son siyasar da ke haɗa kan mutane maimakon rarraba su, da shugabannin da ke samar da hanyoyin magance matsalolin da suke fuskanta.

Kara karanta wannan

Abdul El Sayed: Musulmi na farko ya lashe zaben sanata a Amurka

Shugaba Barrack Obama
Barrack Obama a wajen yakin neman zabe. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Abin da Barrack Obama ya fada a X

A cikin saƙon da ya fitar a X, tsohon shugaban ya ce nasarar da jam'iyyar ta samu ta yiwu ne saboda jajircewar 'yan takara nagari da suka tsaya takara a sassa daban-daban na ƙasar.

Ya ce wasu daga cikin 'yan takarar sun fito ne daga yankunan da a baya ake ganin ba za su iya samun nasara ba.

Obama ya bayyana cewa duk da bambancin asalinsu da ra'ayoyinsu na siyasa, 'yan takarar sun haɗu a kan wasu manufofi, ciki har da hidimtawa jama'a da fifita muradun al'ummomin da suke wakilta.

Obama ya gode wa jama'an Amurka

Tsohon shugaban ya kuma nuna godiya ga dubban jami'an zaɓe da masu aikin sa kai daga jam'iyyun siyasa daban-daban da suka taimaka wajen gudanar da zaɓen.

Ya ce gudunmawarsu ta taimaka wajen tabbatar da gudanar da zaɓen cikin tsari, yana mai cewa gudanar da zaɓe na daga cikin muhimman ayyukan dimokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

Yadda Iran ta 'jawo wa' Trump faduwa zabe a Amurka, ya ce ya yi mamaki

Shugaba Donald Trump
Donald Trump a wajen kamfen a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kiran Obama ga 'yan Democrat

Obama ya jaddada cewa duk da cewa gwamnatin Trump za ta ci gaba da mulki na wasu shekaru biyu, wajibi ne 'yan jam'iyyar Democrat su fara aiki domin kawo sauye-sauye a inda suke da ikon yin hakan.

Ya ce:

“Yanzu aikinmu shi ne mu himmatu wajen gudanar da ayyukan da ke gabanmu, mu kawo sauye-sauye a duk inda muke da ikon yin hakan, mu hana ƙarin ɓarna da kuma aza harsashin gina kyakkyawar makoma.”

Ya ƙara da cewa ya kamata jam'iyyar ta mayar da hankali wajen amfani da damar da ta samu a majalisun dokoki domin kare muradun jama'a.

Zabe: Donald Trump ya zargi Iran

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Donald Trump ya ce yaƙin da ƙasarsa ta shiga da Iran na daga cikin dalilan da suka janyo wa jam'iyyar Republican rashin nasara.

Trump ya bayyana cewa ya yi mamakin sakamakon zaɓen, domin yana tunanin 'yan takarar jam'iyyarsa za su samu nasara fiye da haka.

Sai dai ya ce duk da asarar da jam'iyyarsa ta yi, yaƙin Iran zai fi muhimmanci a tarihi saboda ba za a bar ƙasar ta mallaki makamin nukiliya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng