Wata Sabuwa: Dan Majalisar Amurka Ya Sake Dauko Batun Zargin Kisan Kiristoci a Najeriya
- Dan majalisar wakilan Amurka, Riley Moore, ya ce Kiristoci na ci gaba da fuskantar mummunan tashin hankali a Najeriya
- Moore ya yabawa matakin Shugaba Donald Trump na sake sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ke da matsala kan 'yancin addini
- Gwamnatin Najeriya ta sha yin watsi da ikirarin cewa matsalar tsaro a kasar cin zarafin Kiristoci ne kawai, tana mai cewa ta shafi Musulmi da Kiristoci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Ɗan majalisar wakilan Amurka, Riley Moore, ya sake zargin Najeriya da tauye hakkin kiristoci ta hanyar jefa su cikin mummunan yanayi.
Moore ya yi zargin cewa har yanzu Kiristoci a Najeriya na ci gaba da fuskantar mummunan tashin hankali, shekara guda bayan da Amurka ta sanya kasar cikin jerin kasashen da take zargi da tauye 'yancin addini (CPC).

Kara karanta wannan
An kama mutum 3 kan zargin ƙona motar yan tawagar yakin neman zaben jam'iyyar APC

Source: Twitter
Moore ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a dandalin X, domin tunawa da cikar shekara guda da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake ayyana Najeriya a matsayin kasa da ake da damuwa kan 'yancin addini.
Abin da ɗan majalisar Amurka ya ce
Moore ya rubuta cewa:
“Kiristoci a Najeriya da sauran sassan duniya na ci gaba da fuskantar tashin hankali mai muni. A wannan rana, dole ne mu sake himmatuwa wajen kare Kiristoci a Najeriya da duk inda suke fuskantar tsanantawa.”
Dan majalisar ta Amurka ya yi wannan tsokaci ne yayin da yake nazarin tasirin ayyana Najeriya a matsayin CPC.
Ya ce matakin da Shugaba Trump ya dauka ya dace, tare da kokarin 'yan jam'iyyar Republican a kwamitin kasafin kudi na Majalisar Wakilai ta Amurka na sanya sharudda kan tallafin da ake bai wa Najeriya da kuma bukatar daukar matakan kare Kiristoci.
Moore ya yabawa kokarin Amurka
Moore ya ce shugabancin Trump mai jajircewa da daukar matakai cikin gaggawa, kokarin 'yan Republican a kwamitin kasafin kudi na Majalisar Wakilai da masu rajin kare hakkin bil'adama sun fara haifar da sauyi.
Ya ce:
“Mun ga Kirsimeti na farko ba tare da kisan Kiristoci ba, a cikin shekarun baya-bayan nan.
"Akwai sauran ayyuka da yawa da ya kamata a yi, amma gwamnatin Najeriya ta nuna alamun shirinta na magance tashin hankalin da ake yi wa 'yan'uwanmu cikin Almasihu."
Sai dai ya yabawa kokarin gwamnatin tarayya, yana mai cewa Abuja ta nuna alamun shirinta na magance matsalar tashin hankali.
Tarihin sanya Najeriya cikin CPC
A shekarar 2020 ne Amurka ta fara ayyana Najeriya a matsayin kasa mai matukar damuwa kan 'yancin addini bisa zargin take hakkin 'yancin addini.

Source: Getty Images
Matsayin CPC, wanda dokar Amurka kan 'yancin addini ta tanada, yana bai wa gwamnatin Washington damar daukar matakai kan kasashen da ake zargi da aikata ko amincewa da take hakkin 'yancin addini cikin tsari.
Matakan sun hada da kakaba takunkumi, takaita tallafi da kuma matsin lamba ta fuskar diflomasiyya.
Moore na son a bar Najeriya a CPC
Kun ji cewa ɗan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya dage cewa bai kamata Amurka ta cire Najeriya daga jerin ƙasashen da take zargi da tauye yancin addini (CPC) ba.
Riley Moore ya ce karuwar kashe Kiristoci a yankin Arewa ta Tsakiya ya nuna akwai buƙatar ci gaba da matsa wa Najeriya lamba
Asali: Legit.ng

