Amurka Za Ta Daina Babban Gatan da Take Yi Wa Israila, Trump Fadi Lokaci
- Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya amince da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu cewa Washington za ta daina biyan Isra’ila tallafin dala biliyan huɗu duk shekara.
- Trump ya bayyana lokacin da yarjejeniyar za ta fara aiki daga, amma ya ce Amurka za ta taimaka wa Isra’ila idan ta buƙaci hakan
- Majalisar Wakilan Amurka ta ƙi amincewa da wani ƙudurin dakatar da tallafin Isra’ila a watan Yuli, inda aka kada ƙuri’a 314 kan 104.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Florida, Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ya cimma yarjejeniya da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu.
Shugaba Trump ya bayyana cewa ƙasarsa za ta dakatar da bayar da tallafin kuɗi ga Isra’ila daga ƙarshen shekarar 2026.

Source: Getty Images
Trump ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar Fox News, a cikin shirin Fox and Friends, bayan fara zaɓen tsakiyar wa’adin mulki a Amurka.
Ya ce Amurka na bai wa Isra’ila tallafin dala biliyan huɗu a kowace shekara, amma shi da Netanyahu sun cimma yarjejeniya watanni da suka gabata domin dakatar da wannan biyan kuɗi.
Trump ya bayyana yarjejeniya da Netanyahu
Da yake karin haske kan batun, Trump ya ce:
"Dangane da biyan kuɗin Isra’ila kuwa, ni da Bibi Netanyahu mun cimma yarjejeniya cewa muna ba Isra’ila dala biliyan 4 a shekara, kuma mun cimma yarjejeniya watanni da suka gabata cewa za mu dakatar da hakan.
“Mun riga mun amince cewa daga ƙarshen wannan shekara ba za mu ƙara biyan Isra’ila kuɗi ba. Amma za mu taimaka wa Isra’ila idan ta buƙaci taimako.”
Sai dai har yanzu ba a bayyana takamaiman irin tallafin da Trump yake magana a kai ba, ko kuma ko yarjejeniyar ta shafi dukkan nau’ukan taimakon da Amurka ke bai wa Isra’ila.
Tallafin Amurka ga Isra’ila ya jawo muhawara
Batun tallafin soji da Amurka ke bai wa Isra’ila, da kuma gudummawar kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe daga masu goyon bayan Isra’ila ga ’yan siyasar Amurka, ya zama babban abin muhawara tsakanin ’yan jam’iyyun Democrat da Republican a wannan shekara.
A cikin ’yan shekarun nan, wasu manyan ’yan siyasar Amurka sun fara sukar manufofin Isra’ila a bainar jama’a. Wannan ya nuna sauyi daga matsayin da jam’iyyun Democrat da Republican suka daɗe suna ɗauka na goyon bayan Isra’ila.
Majalisar Wakilai ta ƙi ƙudurin dakatar da tallafin
Tashar Aljazeera ta ce a watan Yuli, Majalisar Wakilan Amurka ta ƙi amincewa da wani ƙuduri da ke neman dakatar da tallafin da ake bai wa Isra’ila.
Duk da cewa kusan rabin ’yan majalisar Democrat sun goyi bayan ƙudurin, bai samu rinjaye ba. Wannan na zuwa ne yayin da ake samun ƙarin saɓani tsakanin masu ra’ayin ci gaba a Amurka da Isra’ila kan yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza, wanda masu suka ke dangantawa da kisan kare dangi.
An kada ƙuri’a 314 domin ƙin amincewa da ƙudurin, yayin da ’yan majalisa 104 suka goyi bayansa. Ƙudurin, wanda ɗan majalisa Thomas Massie mai wakiltar jihar Kentucky ya gabatar a matsayin gyara ga kudirin kashe kuɗaɗen Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, ya nemi a yanke tallafin ga Isra’ila.
Massie, ɗan jam’iyyar Republican, na daga cikin ’yan siyasar Amurka da suka fito fili suna sukar manufofin ƙasarsu a yankin Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
Trump ya yi magana kan Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa dakarun kasarsa sun lalata mafi yawan karfin sojin Iran.
Shugaba Donald Trump ya ce amma har yanzu akwai wasu cibiyoyi daya ko biyu da suke bukatar kai wa hari.
Asali: Legit.ng


