Babbar Magana: Trump Ya Fadi Abin da Ya Rage Amurka Ta Yi a Iran

Babbar Magana: Trump Ya Fadi Abin da Ya Rage Amurka Ta Yi a Iran

  • Donald Trump ya ce Amurka ta lalata mafi yawan karfin sojin Iran da shirinta na nukiliya, amma akwai abin da ya rage ta yi
  • Jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei, ya gargadi Amurka da Isra’ila kan sake kai wa kasarsa hari, yana mai cewa za su fuskanci martani mai tsanani
  • Ministan Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce Trump bai yanke shawarar sake kai wa Iran hari ba, kuma Washington a shirye take ta bi hanyar diflomasiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Florida, Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa dakarun kasarsa sun lalata mafi yawan karfin sojin Iran

Shugaba Trump ya ce amma har yanzu akwai wasu cibiyoyi daya ko biyu da suke bukatar kai wa hari.

Trump ya yi maganar kai wa Iran hari
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a fadar White House Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, yayin da gwamnatin Iran ta yi gargadin cewa za ta mayar da martani mai tsanani idan Amurka da Isra’ila suka sake kai mata hari, cewar rahoton tashar CBS.

Kara karanta wannan

Akwai ƙura: Mojtaba Khamenei ya gargaɗi Amurka da Isra'ila kan sake kai hari ƙasar Iran

Shugaban ya kuma ce tattaunawar da ake yi da Iran domin kawo karshen yakin da Amurka da Isra’ila suka fara a watan Fabrairun 2026 na tafiya yadda ya kamata, duk da cewa bai amince da amincin gwamnatin Tehran ba.

Trump ya yi magana kan cibiyoyin nukiliyar Iran

Da yake magana da manema labarai a gidansa da ke jihar Florida, Trump ya ce Amurka ba ta cikin gaggawar sake kai wa Iran hari saboda ta riga ta raunana karfin sojinta da shirinta na nukiliya.

"Mun lalata shirinsu na nukiliya. Har yanzu akwai wasu cibiyoyi daya ko biyu da ya kamata mu kula da su, amma za mu iya yin hakan cikin mintuna 10." In ji shi.

Trump ya kuma ambaci wani wuri da ake kira Pickaxe Mountain, wanda ake zargin yana dauke da wata cibiyar nukiliya da aka gina karkashin kasa.

Ya ce Amurka za ta iya kai wa wurin hari cikin kankanin lokaci idan ta yanke shawarar yin hakan.

Kara karanta wannan

Jerin labaran karya da suke yawo a yanar gizo da za a iya dauka gaskiya ne

Sai dai gwamnatin Iran ta musanta cewa tana gudanar da wani aikin nukiliya a wannan wuri.

Amurka ba ta yanke shawarar sake kai hari ba

Tun da farko, Ministan Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana cewa Trump bai yanke shawarar sake kai hare-hare kan Iran ba.

Rubio ya ce duk da rikicin da ke tsakanin kasashen biyu, har yanzu Amurka a shirye take ta bi hanyar diflomasiyya domin samar da mafita.

Wannan na zuwa ne yayin da ake samun karuwar barazanar sake barkewar fada tsakanin Amurka da Isra’ila a gefe guda, da Iran a daya bangaren.

Trump ya taba yin gargadin cewa Amurka za ta iya sake kai wa Iran hari bayan zaben tsakiyar wa'adin majalisar dokokin Amurka da aka gudanar a wannan makon.

Haka kuma, Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi magana kan abin da ya kira babbar dama ta tarihi da ba kasafai ake samu ba domin kifar da gwamnatin Iran.

Trump ya yi barazana ga Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An sauke babban soja a Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya sallami babban jami’in da ke kula da tsare-tsare da manufofin dabarun sojin ƙasar, Laftanar Janar Brett Sylvia.

Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ce ta bayyana cewa an cire Sylvia daga muƙaminsa na daraktan tsare-tsare da manufofin dabarun rundunar hafsoshin sojin Amurka, wanda aka fi sani da J5.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng