Shugaban Iran Ya Yi Gargadi kan Barkewar Sabon Yaki tsakanin Kasarsa da Amurka
- Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa sake barkewar yaƙi ba zai amfani kowa ba
- Babban mai shiga tsakani na Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya ce ƙasar a shirye take ta fuskanci yaƙi
- Rahotanni sun ce Amurka ta kai hare-hare a tsibirin Qeshm da ke mashigar ruwan Hormuz, yayin da Donald Trump ya nuna cewa yarjejeniya da Iran na iya yiwuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa sake barkewar yaƙi tsakanin ƙasarsa da Amurka ba zai amfani kowa ba.
Kalaman Pezeshkian na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan rahotannin cewa sojojin Amurka sun kai hare-hare a wani tsibirin Iran da ke mashigar ruwan Hormuz.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa shugaban na kasar Iran ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 3 ga watan Nuwamban 2026.
Iran ta ce tana shirye-shiryen kare kanta
Babban jami’in Iran da ke jagorantar tattaunawa da Amurka, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya bayyana cewa ƙasarsa a shirye take ta fuskanci yaƙi, kuma tana da yatsanta a kan maƙunnin bindiga.
Haka kuma, mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Kazem Gharibabadi, ya ce ƙasarsa na da haƙƙin kare kanta bisa ƙa'ida bayan hare-haren da aka kai.
Sai dai Pezeshkian ya jaddada cewa gwamnatinsa na ci gaba da ƙoƙarin warware rikicin ta hanyar tattaunawa maimakon komawa fagen daga.
Ya ce babu wanda zai amfana idan aka sake kunna wutar yaƙin, yana mai cewa jagoran addini na ƙasar, Ali Khamenei, ya bai wa gwamnati ƙarin ikon tattaunawa kan wasu batutuwan da a baya ba a yarda a tattauna kansu ba.
Amurka ta kai hari tsibirin Qeshm
Jaridun The Wall Street Journal, CNN, The New York Times da wasu kafafen yaɗa labarai sun rawaito cewa hare-haren Amurka sun shafi tsibirin Qeshm da ke mashigar ruwan Hormuz.

Kara karanta wannan
An fara batun Tinubu ya je Umrah ne don neman kuri'un 'yan Arewa, hadiminsa ya magantu
Wannan mashigar ruwa na daga cikin wuraren da rikicin Gabas ta Tsakiya ya fi shafa, kuma yaƙin ya haddasa tangarɗa a kasuwannin duniya.
Wasu jami’an Amurka da ba a bayyana sunayensu ba, waɗanda kafafen yaɗa labaran suka ambata, sun ce hare-haren na da manufar kare kai.
Jaridar The Wall Street Journal ta kuma bayyana cewa wannan sabon hari na cikin jerin hare-haren da Amurka ta kai a baya ba tare da sanar da su a hukumance ba.
Rikicin Amurka da Iran ya shafi duniya
Amurka da Isra’ila sun fara yaƙin da Iran ne ta hanyar kai jerin hare-hare masu ƙarfi a ƙarshen watan Fabrairun 2026.
Tun daga lokacin, rikicin ya shafe watanni yana gudana ba tare da ɗaya daga cikin ɓangarorin ya samu gagarumar nasara ko warware matsalar ba.
Rahoton harin da aka kai tsibirin Qeshm ya fito ne sa’o’i kaɗan bayan Trump ya nuna cewa yarjejeniya da Iran na iya yiwuwa.
A halin da ake ciki, zaɓen tsakiyar wa’adin mulkin Amurka na gudana ne a lokacin da rashin jin daɗin jama’a kan yaƙin da kuma hauhawar farashin kayayyaki da ya haddasa ke cikin manyan batutuwan da suka mamaye siyasar ƙasar.

Source: Twitter
Batun kashe shugabannin Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya ce yana buƙatar dakatar da kashe shugabannin Iran.
Shugaba Trump ya ce yana bukatar dakatar da kashe shugabannin ne domin ya iya gano waɗanda ƙasarsa ke tattaunawa da su.
Asali: Legit.ng

