Akwai Kura: Mojtaba Khamenei Ya Gargadi Amurka da Isra'ila kan Sake Kai Hari Kasar Iran
- Jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei ya gargadi Amurka da Isra'ila su guji koma yaki da kasar Musulunci
- Khamenei ya umarci manyan kwamandojin sojin Iran da su shirya maida martani kan duk wata barazana ko hari daga kasashen biyu
- Bayanai sun nuna cewa jagoran Iran ya bayyana haka a ne a wurin wani taro da kwamandojin Iran bayan barazanar Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Babban jagoran kasar Iran, Mojtaba Khamenei, a ranar Asabar ya yi gargadi ga kasar Amurka da Isra'ila kan komawa fagen yaki.
Khamenei ya gargadi Amurka ta Isra'ila da kada su sake kai hare-hare kasar Musulunci ta Iran, yana mai cewa hakan zai zama yunkurin sake komawa fagen yaki.

Source: Getty Images
Al-Jazeera ta ruwaito cewa jagoran ya yi wannana gargadi ne a wata sanarwa ta rubuce da ya fitar biyo bayan barazanar kasashen biyu na na yiwuwar cigaba da kai hare-hare.
Iran ta ja kunnen Amurka da Isra'ila
Sanarwar da aka fitar a shafinsa na intanet, wacce aka danganta ga Khamenei, ta ce:
“Idan har abokan gaba suka sake kaddamar da hare-hare na ta’addanci, to rundunonin tsaron Jamhuriyar Musulunci da al’ummar Iran ne za su tantance lokaci da kuma sharuddan kawo karshen yakin.”
An fitar da wadannan maganganu ne yayin wani taro da aka rahoto cewa an yi tsakanin Khamenei da manyan kwamandojin sojin Iran.
Taron ya hada da babban hafsan hafsoshin sojojin kasar, Ali Abdollahi, babban hafsan sojojin kasa, Amir Hatami, da kuma kwamandan rundunar juyin juya hali, Ahmad Vahidi.
Wannan ne taronsu na farko da aka fara rahoto tsakanin jagoran Iran da kwamandojin tun bayan nada shi a mukamin.
Ba a taba ganin Khamenei a idon jama'a ba tun bayan da ya zama babban jagora, biyo bayan kisan mahaifinsa, Ayatollah Ali Khamenei, a hare-haren da Amurka da Israel suka kai a farkon yakin Gabas ta Tsakiya a watan Fabrairu.
Khamenei ya umarci kwamandojin Iran
Bisa la’akari da sanarwar, Khamenei ya umarci kwamandojin da su tabbatar da cewa “kowane irin mataki ko nau'in barazana dole ne a mayar da martani nan take, mai karfi, kuma ba tare da an takaita shi a wani wuri na musamman ba.”
Sanarwar ta kuma bayyana cewa Khamenei ya umarci kwamandojin da su sabunta jerin sunayen abubuwan da za su zama abin harin Iran, kamar yadda Vanguard ta kawo.

Source: UGC
Yakin ya fara ne a ranar 28 ga watan Fabrairu da hare-haren Amurka da Israel suka kai kan Iran, inda ita ma ta mayar da martani cikin sauri da kai hare-hare kan kasashe masu makwabtaka da yankin.
Sanarwar babban jagoran ta zo ne yayin da ake ci gaba da kokarin diflomasiyya domin dakile sake barkewar fada.
Shirin sojojin Amurka kan Iran
Kun ji cewa sojojin Amurka na tsara kai hare-hare kan cibiyoyin makamashi da na nukiliyar Iran, da amfani da bam mai hadari da ake kira “uwar bama-bamai."
Babu wata alama mai ƙarfi da ke nuna cewa Amurka da Iran sun kusa cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen rikicin bayan fiye da watanni shida ana kai hare-haren bama-bamai.
Asali: Legit.ng

