Amurka na Shirin Sake Kai Sababbin Hare Hare a Iran? Trump Ya Yi Bayani
- Donald Trump ya ce Amurka ba za ta kai wa Iran hari kafin zaɓen tsakiyar wa’adi na ranar 3 ga Nuwamba ba, duk da ci gaba da takun saka
- Shugaban na Amurka ya bayyana cewa Washington na gudanar da tattaunawa mai kyau da Iran, yayin da takunkumin hana zirga-zirga zai ci gaba
- Farashin ɗanyen mai ya haura dala 105.88 kan kowace ganga a ranar Alhamis, sakamakon fargabar sabon hari da tashin hankali a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan batun sake kai sababbin hare-hare a Iran.
Trump ya ce ƙasarsa ba za ta kai wa Iran hari ba kafin zaɓen tsakiyar wa’adin Amurka da za a gudanar ranar 3 ga Nuwamba, yana mai cewa ana tattaunawa mai kyau da Tehran.

Kara karanta wannan
Bayan fetur, Gwamnatin tarayya na shirin rage hauhawar farashin muhimman kayayyaki

Source: Getty Images
Trump ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoban 2026 ta shafinsa na Truth Social, bayan rahotannin kafofin yaɗa labarai kan yiwuwar Amurka ta sake kai wa Iran hari sun haddasa tashin farashin ɗanyen mai.
Trump ya ce ana tattaunawa da Iran
Trump ya ce duk da cewa Iran na cikin mawuyacin hali ta fuskar tattalin arziƙi da soji, Amurka ba za ta kai mata hari ba kafin zaɓen tsakiyar wa’adi.
Ya rubuta cewa:
“Ina so in bayyana wa kowa cewa, duk da cewa Iran na cikin mummunan hali ta fuskar tattalin arziƙi da soji, kuma za a ci gaba da aiwatar da shirin killace ta, ba za mu kai wa Iran hari a kowane lokaci kafin zaɓen tsakiyar wa’adi ba.”
"Muna gudanar da tattaunawa mai amfani da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.”
Rahotanni sun ce Pentagon na tsara yiwuwar kai hari
Mujallar The Atlantic ta ruwaito ranar Laraba cewa Fadar White House ta nemi Ma’aikatar Tsaron Amurka, Pentagon, ta tsara hanyoyin kai hari kan wasu wurare a Iran da za a iya amfani da su kafin zaɓen.

Kara karanta wannan
Bayan rage farashi, Gwamnatin Tinubu ta yi bayani kan yiwuwar dawo da tallafin fetur kafin 2027
Jaridar The New York Times ta kuma ruwaito ranar Alhamis cewa ana ci gaba da tsara waɗannan shirye-shirye duk da rashin cikakken matsaya daga Trump kan batun.
Sai dai sanarwar Trump ta cewa ba za a kai hari kafin zaɓen ba ta zo ne a lokacin da ake samun fargabar ƙarin rikici a yankin.
Trump ya ce Amurka ta yi nasara a yaƙin
A makonnin baya-bayan nan, Trump ya sha nanata cewa Amurka ta yi nasara a yaƙin Iran, duk da cewa tashin hankali bai ƙare ba.
Haka kuma, an samu barazanar tsaro a baya-bayan nan da ta tilasta janye jiragen yaƙin Amurka daga wani sansani a Ingila.
Sanarwar Trump ta cewa ba za a kai wa Iran hari kafin zaɓen ba ta zo ne yayin da ake ci gaba da sa ido kan tattaunawar diflomasiyya da kuma tasirin rikicin kan kasuwannin mai na duniya.

Source: Getty Images
Amurka ta kori jami'an Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa Amurka ta kori mambobin tawagar Iran biyu da suka halarci babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya bayan sun ƙi bin umarnin barin ƙasar.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayyana korar jami'an na Iran a ranar Asabar, 3 ga watan Oktoban shekarar 2026.
Asali: Legit.ng