Rigima Sabuwa: Sabon Shirin da Amurka da Israila Ke Yi kan Iran
- Amurka da Isra’ila sun tsara yiwuwar sake kai hare-hare kan Iran bayan zaɓen tsakiyar wa’adin Amurka
- Ana sa ran hare-haren za su shafi cibiyoyin makamashi, wuraren nukiliya da ma’ajiyar makaman linzami da jiragen sama marasa matuƙa na Iran
- Iran ta yi barazanar mayar da martani ta hanyar faɗaɗa wuraren da za ta kai wa hari, yayin da tattaunawar diflomasiyya kan shirin nukiliyarta ke ci gaba da fuskantar cikas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Sojojin Amurka da Isra’ila sun tsara wasu takamaiman tsare-tsaren sake kai hare-hare kan Iran bayan zaɓen tsakiyar wa’adin Amurka.
Wasu jami’an Amurka da wasu mutanen da aka sanar da su bayanan tattaunawar shirye-shiryen sojoji suka bayyana hakan.

Source: Getty Images
Rahoton New York Times ya bayyana cewa yayin da ake ci gaba da tsara wani gajeren farmaki mai tsanani, sojojin ƙasashen biyu sun ƙara yawan atisayen soji, ciki har da shawagin jiragen yaƙi a sararin samaniyar Iraki domin atisayen dabarun kai hare-hare.
Wasu jami’an Amurka sun Ministan Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya gana da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, a Isra’ila a wannan makon domin tattauna yiwuwar sababbin hare-haren.
Dukkan jami’an da aka yi hira da su game da wannan rahoto sun nemi a ɓoye sunayensu domin ba su iya magana a fili kan tsare-tsaren soji.
Wuraren da za a kai wa hari
Rahoton ya ce wuraren da za a iya kai wa hari sun haɗa da cibiyoyin samar da makamashi na Iran, wuraren nukiliya, da kuma ma’ajiyar makaman linzami da jiragen sama marasa matuƙa.
Wasu jami’an sun yi imanin cewa wani babban zagaye na hare-hare zai iya ƙara tsananta matsin tattalin arziki a Iran, har ya tilasta wa ƙasar sassauci a tattaunawar diflomasiyya bayan kusan watanni takwas na rikici.
Wasu masu tsara dabarun soji na Amurka sun yi imanin cewa farmakin kwanaki uku mai tsanani zai iya jawo babbar illa ga tattalin arzikin Iran, ta yadda zai sauya matsayinta a tattaunawar.
Sai dai ba a tabbatar da cewa Shugaba Donald Trump ya amince da aiwatar da wannan shiri ba.
Akwai shakku kan nasarar sabon farmakin
Duk da shirye-shiryen, rahoton ya ce akwai dalilan da za su sa a yi shakku kan ko sake fara yaƙin zai haifar da sakamako mafi kyau fiye da zagayen farko na hare-haren Amurka da Isra’ila tsakanin Fabrairu da Afrilu.
Hare-haren da aka kai a wancan lokaci sun taimaka wajen ƙara farashin makamashi da hauhawar farashin kayayyaki a duniya, raunana tsaro a Gabas ta Tsakiya, tare da rage yawan makaman kariya da Pentagon ke da su domin tare makamai masu linzami.
Haka kuma, har yanzu ba a san ko Trump zai amince da sake kai hare-haren ba. A cewar rahoton, a lokuta da dama a wannan shekara ya dakatar da tsare-tsaren komawa manyan hare-haren soji, ciki har da a wannan watan, lokacin da sojojin Amurka da Isra’ila suka kusa kammala shirye-shiryen kai hari.
Iran ta yi barazana
Jami’an Iran sun yi alƙawarin cewa idan aka sake kai musu hari, za su faɗaɗa wuraren da za su kai wa hari fiye da jiragen kasuwanci da cibiyoyin makamashi a yankin.
A cewar rahoton, Iran ta kuma yi barazanar kai hari kan cibiyoyin adana bayanai na kwamfuta da igiyoyin intanet da aka shimfiɗa ƙarƙashin teku.
Jami’an Iran sun jaddada cewa idan aka sake fara faɗa, ba zai zama yaƙi mai saurin ƙarewa ko wanda za a takaita shi ga wasu wurare kaɗan ba.

Source: Getty Images
Trump ya kori kakakinsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sallami kakakinsa ta fadar White House, Katie Zacharia.
Trump ya kore ta ne bayan kwanaki biyar kacal da fara aiki, sakamakon suka da ta fuskanta bayan fitowarta ta farko a gaban manema labarai.
Asali: Legit.ng


