Elon Musk Ya Koma Matsayinsa a Duniya da Dukiyarsa Ta Karu da Naira Tiriliyan 117
- A cikin makon nan Elon Musk ya sake zama attajirin duniya na farko da dukiyarsa ta haura dala tiriliyan ɗaya
- Dukiyarsa ta ƙaru da dala biliyan 88, inda ta kai dala tiriliyan 1.013 sakamakon tashin hannun jarin SpaceX da Tesla
- Hannun jarin SpaceX ya tashi sama da 10% bayan samun ribar da ta zarce hasashen masana, na Tesla ya tashi da 3%
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
America - Elon Musk ya sake komawa matsayinsa na mutum na farko a duniya da ɗinbin dukiyarsa ta haura dala tiriliyan ɗaya.
A safiyar Laraba attajirin ɗan kasuwar ya kafa tarihi a dalilin tashin darajar hannun jarin kamfanoninsa na SpaceX da Tesla.

Source: Getty Images
Arzikin Elon Musk ya koma gidan jiya
Rahoton Forbes ya nuna cewa hajarsa ta ƙaru da kusan dala biliyan 88 cikin sa'a ɗaya kacal bayan buɗe kasuwar hannayen jari.
A kuɗin Najeriya, Musk ya tashi da sama da Naira tiriliyan 117 kenan a cikin ɗan lokaci kaɗan.
A lissafin da mujallar ta ke yi, dukiyar Musk ta kai dala tiriliyan 1.013 da misalin ƙarfe 10:30 na safiyar 21 ga watan Oktoba 2026.
Ya aka yi dukiyar Elon Musk ta ƙaru?
Ƙarin dukiyar nasa ya biyo bayan tashin darajar hannun jarin SpaceX da sama da 10%.
Hakan ya faru ne bayan kamfanin ya fitar da rahoton kuɗinsa na zango na uku na shekarar, wanda ya zarce hasashen masana.
Haka kuma, darajar hannun jarin Tesla ta ƙaru da sama da 3% gabanin fitar da rahoton kuɗin kamfanin na zangon da ya wuce.
Tashin darajar hannun jarin ya biyo bayan tabbatarwar Musk cewa kamfanonin SpaceX da Tesla na duba yiwuwar haɗewa.
Musk mai shekara 55 da haihuwa ya fara zama mutum na farko a duniya da dukiyarsa ta kai dala tiriliyan a ranar 12 ga Yuni 2026.
Arzikin Elon Musk ya saba raguwa
Bayan SpaceX ta shiga kasuwar hannayen jari, ya rika rasa wannan matsayi duk da cewa babu wani attajirin da ya kama kafarsa.
An ce a makon da ya gabata, ya sake faɗowa ƙasa daga wannan matsayi bayan darajar hannun jarin SpaceX ta ragu da sama da 3.5%.
Sakamakon sauyin darajar hannayen jarin kamfanoninsa, Musk ya ba $1.01tr baya a ranar.
Babu mai kudin da ya kama kafar Musk
Ko da Forbes ta rahoto dukiyar attajirin ta sake sauka daga baya, bai da sa'a a sahun masu kudi.
Jeff Bezos wanda shi ne attajiri na biyu a duniya yana da $380bn ne a yau. Kusan ɗaya bisa ukun abin da Musk yake da shi kenan.
Wanda yake biye da shi a baya wani ‘dan Amurkan ne, Larry Page wanda ake hasashen ya mallaki kimanin dala biliyan 280 a Oktoba.

Source: Getty Images
Hasashen Elon Musk ya rage wa kudi muhimmanci
An ji labari attajirin duniya Elon Musk ya yi hasashen cewa nan da shekaru 10 (a 2036) kuɗi za su rage tasiri sosai a duniya.
Hakan zai faru ne sakamakon gagarumin ci gaban fasahar AI da mutum-mutumi da za su riƙa samar da kaya da ayyuka da yawa.
Ya ce fasahar za ta haifar da babban wadatar rayuwa ga kowa, inda na'urori za su riƙa yin yawancin ayyukan samar da arziki.
Asali: Legit.ng


