Matsala Ta Faru: Cutar Ebola Ta Dawo Najeriya, an Ɗauki Tsauraran Matakai
- Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da bullar cutar Ebola guda ɗaya a Abuja, inda aka gano mutum 44 da suka yi hulɗa da majinyaciyar
- Ministan Lafiya, Muhammad Ali Pate, ya ce wata mata da ta dawo Najeriya daga Uganda ce ta kamu, kuma yanzu tana keɓe tana samun kulawa
- Gwamnati ta fara bin diddigin waɗanda suka yi hulɗa da ita, tare da ƙarfafa matakan kariya, tana kira ga jama'a su kula da alamomin cutar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da bullar cutar Ebola guda ɗaya a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Majiyoyi suka ce an fara binciken waɗanda suka yi hulɗa da majinyaciyar saboda dakile yaduwarta.
Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama'a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Talata, 20 ga Oktoba, 2026, bayan sakamakon gwaje-gwajen dakin bincike ya tabbatar da cutar, cewar Punch.
An gano mutum 44 da suka yi kusanci da ita, a wani mataki na hana cutar yaɗuwa zuwa ga sauran mutane.
Sanarwar ta ce wata mata da ta dawo Najeriya daga Uganda ta jirgin sama na ƙasa da ƙasa, an kwantar da ita a wani asibiti mai zaman kansa a Abuja, inda aka yi mata magani na wasu kwanaki kafin a tabbatar da tana ɗauke da cutar.
A halin yanzu, an keɓe matar kuma tana samun kulawar likitoci.
Ma'aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama'a ta Tarayya, Cibiyar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC), da Hukumar Kula da Lafiya ta Abuja, suna aiki tare da sauran hukumomin da abin ya shafa domin shawo kan cutar da hana yaɗuwarta.
Gwamnati ta bayyana cewa jami'an kula da lafiyar jama'a sun fara bin diddigin mutane 44 da aka gano sun yi hulɗa da majinyaciyar.
Haka kuma, jami'an na ƙoƙarin gano wasu mutanen da wataƙila suka kamu da cutar, ciki har da ma'aikatan lafiya, majinyata, masu kula da marasa lafiya da mutanen da suka yi tafiya tare da ita.
An kuma ƙara tsaurara sa ido kan cututtuka, yayin da ake ba asibitin da aka yi wa matar magani tallafin gaggawa domin inganta matakan kariya daga yaɗuwar cututtuka.
Gwamnati ta buƙaci asibitocin gwamnati da masu zaman kansu a faɗin ƙasar su kasance cikin shirin ko-ta-kwana domin tunkarar duk wata alamar bullar cutar.
Ta umarci ma'aikatan lafiya su riƙa lura da alamomin cutar, gano waɗanda ake zargi da wuri, keɓe su, bin ƙa'idojin kariya daga kamuwa da cututtuka da kuma sanar da hukumomin lafiya nan take idan an samu wanda ake zargi.
Ministan ya shawarci 'yan Najeriya su kwantar da hankalinsu tare da bin matakan kariya, ciki har da wanke hannu akai-akai da kuma guje wa taɓa jini ko sauran ruwan jikin mutumin da ake zargin yana ɗauke da cutar Ebola.
Alamomin cutar Ebola
Ya bayyana cewa alamomin da ya kamata jama'a su lura da su sun haɗa da zazzaɓi, matsananciyar kasala, ciwon kai, amai da gudawa, musamman ga mutanen da wataƙila sun yi hulɗa da cutar.
Sanarwar ta shawarci duk wanda ya fara nuna alamomin cutar da ya guji kusantar sauran mutane, sannan ya kira hukumomin kula da lafiyar jama'a domin samun shawarwari kafin zuwa asibiti.

Kara karanta wannan
Minista ya ɓallo ruwa a gaban ƙasashen duniya, ya yi maganar da ka iya juyo wa kan Tinubu
Gwamnati ta kuma buƙaci mutanen da jami'an lafiya suka tuntuba yayin binciken waɗanda suka yi hulɗa da majinyaciyar, ciki har da fasinjojin jirgin da wataƙila suka kamu, su bayar da bayanan da ake buƙata tare da bin umarnin hukumomi.
Tabbatar da bullar cutar a Najeriya na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun yaɗuwar Ebola a wasu ƙasashen yankin.
A ranar 6 ga Oktoba, hukumar NCDC ta fitar da sanarwar gargaɗi kan yiwuwar shigo da cutar Najeriya, bayan tabbatar da bullarta a Kenya, wadda ke da alaƙa da barkewar cutar a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa cutar Ebola tana yaɗuwa ta hanyar taɓa jinin ko sauran ruwan jikin mutumin da ya kamu da ita, ko abubuwa da saman da suka gurɓata da cutar.
Mutumin da ya kamu da cutar ba ya yaɗa ta kafin alamominta su bayyana. Lokacin da cutar ke ɗauka kafin bayyanar alamomi yana tsakanin kwanaki biyu zuwa 21.
A shekarar 2014, Najeriya ta yi nasarar shawo kan bullar cutar Ebola bayan wani matafiyi da ya kamu da ita ya shigo ƙasar.
Matakan da aka ɗauka sun haɗa da gano waɗanda suka kamu da wuri, keɓe su, bin diddigin waɗanda suka yi hulɗa da su da kuma haɗin gwiwar hukumomin kula da lafiyar jama'a.
Pate ya kwantar wa 'yan Najeriya da hankali, yana mai cewa ƙasar tana da ƙwarewa da tsarin kula da lafiyar jama'a da za su taimaka wajen shawo kan wannan bullar cutar.
Karin bayani na tafe....
Asali: Legit.ng


