Isra'ila na Shirin Taimaka wa Saudiyya kan Matsalarta, Trump Ya Yi Magana

Isra'ila na Shirin Taimaka wa Saudiyya kan Matsalarta, Trump Ya Yi Magana

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Saudiyya na iya amincewa da taimakon Isra’ila wajen yakar mayakan Houthi a Yemen
  • Trump ya bayyana kwarin gwiwar cewa yarjejeniyar Abraham za ta iya farfadowa, inda Saudiyya za ta shiga domin kulla alakar diflomasiyya da Isra’ila
  • Wannan na zuwa ne yayin da Houthi suka kai hare-hare Saudiyya, inda aka kashe mutane tare da jikkata daruruwan wasu a Riyadh

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa Saudiyya za ta iya amincewa da taimakon Isra’ila a irin yanayin da ake ciki a yanzu.

Trump ya ce hakan zai taimaka wajen yaƙar ’yan tawayen Houthi a Yemen, tare da ƙoƙarin farfaɗo da shirin shigar da ƙasar cikin yarjejeniyar Abraham.

Trump ya magantu kan taimakon Isra'ila a Saudiyya
Shugaban Amurka, Donald Trump tare da Yariman Saudiyya, Muhammad bin Salman, suna tattaunawa a Washington, DC. Hoto: Chip Somodevilla.
Source: Getty Images

Trump ya magantu kan hare-haren Houthi

Kara karanta wannan

"Sun tsorata," Kwankwaso ya gano sasu shirin maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027

Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, inda aka tambaye shi ko ya kamata Saudiyya ta karɓi taimakon da Isra’ila ke bayarwa domin yaƙar Houthi, cewar Al Jazeera.

Da aka tambaye shi ko ya kamata Saudiyya ta karɓi taimakon Isra’ila, Trump ya amsa da cewa:

“Eh, ina ganin ya kamata.”

An kuma tambayi shugaban Amurka ko ya tattauna da Saudiyya kan yiwuwar karɓar taimakon, inda ya ce:

“Ina ganin za su yi hakan. Tabbas, Isra'ila ta taimaka wa Saudiyya sosai, kuma eh, tabbas za su yi hakan.”

Trump ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa yarjejeniyar Abraham za ta iya samun sabon ƙarfi ta hanyar shigar Saudiyya cikin yarjejeniyar.

Da aka tambaye shi ko har yanzu akwai yiwuwar kulla yarjejeniyar da Saudiyya, Trump ya ce:

“Wataƙila fiye da kowane lokaci.”
"Yarjejeniyar Abraham na ɗaya daga cikin manyan nasarorinmu, kuma eh, zan ce wataƙila yanzu ne damar ta fi kowane lokaci.”
Trump ya shawarci Saudiyya kan yaki da Houthi
Shugaba Donald Trump na Amurka a birnin New York. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: Twitter

Goyon bayan da Amurka ke ba Saudiyya

Trump ya kuma bayyana cewa Saudiyya tana farin cikin samun goyon baya daga Isra’ila da kasar Amurka, kamar yadda The Jerusalem Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya sake maganganu kan Atiku, ya tono tsohon tarihi

Ya ce:

“Amma Saudiyya tana farin cikin samun goyon baya daga Isra’ila da kuma mu.”

Saudiyya ba ta kulla dangantakar diflomasiyya da Isra’ila ba, kuma shigar ƙasar cikin yarjejeniyar Abraham na daga cikin manyan manufofin Trump a yankin Gabas ta Tsakiya.

A baya, Trump ya bayyana cewa yarjejeniyar haɗin gwiwar nukiliya ta farar hula tsakanin Amurka da Saudiyya tana da alaƙa da shigar Saudiyya cikin yarjejeniyar Abraham da kuma daidaita dangantakarta da Isra’ila.

Trump ya gargadi Amurkawa a Saudiyya

A baya, an ji cewa Amurka ta gargaɗi ’yan ƙasarta da ke Saudiyya da su guji filin jirgin saman Sarki Khalid da kewaye bayan rahotannin hare-hare.

Ofishin jakadancin Amurka ya yi gargaɗin yiwuwar soke jirage da rufe sararin samaniya, tare da sanya takunkumin zirga-zirga.

Ya kuma shawarci Amurkawa su bi umarnin hukumomi, guji taruka da wuraren haɗari, tare da bibiyar sanarwar tsaro domin kare rayukansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.