Babbar Magana: An Kai Harin da Ya Shafi Sama da Mutane 300 a Saudiyya

Babbar Magana: An Kai Harin da Ya Shafi Sama da Mutane 300 a Saudiyya

  • Hukumomin Saudi Arabiya sun ce aƙalla mutum 12 sun mutu, yayin da wasu 309 suka jikkata a harin da aka kai filin jirgin saman Sarki Khalid da ke Riyadh
  • Waɗanda suka mutu sun haɗa da ’yan Saudiyya, Bangladesh da wasu ƙasashe, ciki har da Amurka, Jordan, Falasɗinu, Siriya, Sudan da Masar
  • Rundunar haɗin gwiwar da Saudiyya ke jagoranta ta yi Allah-wadai da harin, tana mai cewa za ta mayar da martani mai tsauri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Riyadh, Saudiyya - Saudiyya ta bayyana cewa aƙalla mutum 12 sun mutu, yayin da sama da 300 suka jikkata a wani hari da ’yan Houthi na Yemen suka kai.

Mayakan na Houthi sun kai harin ne a filin jirgin saman King Khalid da ke kusa da babban birnin ƙasar, Riyadh.

Kara karanta wannan

Jita jita ta ƙare, an fito da bayanin da ya kamata mutane su sani kan hatsarin jirgin sojoji

Mayakan Houthi sun kai hari a Saudiyya
Hayaki ya tashi a wani bangare na filin jirgin saman King Khalid a Saudiyya Hoto: @anwaribrahim
Source: Getty Images

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Saudiyya (GACA) ta ce harin na ranar Asabar, 10 ga watan Oktoban 2026 ya yi sanadin mutuwar aƙalla ’yan ƙasar Saudiyya huɗu da kuma ’yan Bangladesh biyu, cewar rahoton tashar Aljazeera.

Sauran waɗanda suka mutu sun fito ne daga Amurka, Jordan, Falasɗinu, Siriya, Sudan da Masar, inda kowace ƙasa ta rasa mutum guda.

Hukumar ta ce adadin waɗanda suka jikkata ya kai aƙalla 309. Wasu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali, kuma ana ba su kulawar likitoci a asibitoci.

Harin ya kuma haddasa lalacewar kadarori. Wannan shi ne karo na uku da ’yan Houthi suka kai hari kan filin jirgin saman na ƙasa da ƙasa a cikin makon.

An dakatar da ayyukan filin jirgin saman

A cewar GACA, wani harin da aka kai filin jirgin saman King Khalid ranar Alhamis ya kashe aƙalla ’yan Saudiyya uku, ciki har da matukin jirgin sama.

Kara karanta wannan

Kakar miliyoyin matasa ta yanke saƙa, an fadada shirin tallafin rage talauci a Najeriya

Bayan harin, an dakatar da ayyukan filin jirgin saman na ɗan lokaci domin jami’ai su tantance barnar da aka yi.

Haka kuma, Manjo-Janar Turki al-Maliki, kakakin rundunar haɗin gwiwar da Saudiyy ke jagoranta a yaƙin Yemen, ya tabbatar da cewa wani makami ya faɗa kusa da filin jirgin saman King Fahd da ke Dammam.

Saudiyya ta yi barazanar mayar da martani

Rundunar haɗin gwiwar ta bayyana harin a matsayin babban laifin yaƙi. Al-Maliki ya ce za su mayar da martani mai tsauri kan abin da ya kira harin ta’addanci, bisa ƙa’idojin dokokin jinƙai na yaƙi.

'Yan Houthi sun nuna cewa filin jirgin saman Sarki Khalid da sauran filayen jiragen sama na Saudi Arabiya na cikin manyan wuraren da suke son kai wa hari.

Bayan harin na ranar Asabar, shugaban ofishin yaɗa labaran Houthi ya wallafa a shafin X cewa ƙungiyar ta “rufe filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Riyadh”.

Yaƙi ya ƙara tsananta a Yemen

Hare-haren sun zo ne a daidai lokacin da faɗa ke ƙara tsananta a Yemen, inda dakarun da ke biyayya ga gwamnatin ƙasar da ƙasashen duniya suka amince da ita ke yaƙi da ’yan Houthi da Iran ke goyon baya domin samun iko da ƙasar.

Kara karanta wannan

Yadda aka tono gawar basarake a Kano bayan 'yan bindiga sun kashe shi

Saudiyya ta gudanar da hare-haren sama domin tallafa wa gwamnatin Yemen a yaƙin da take yi a ƙasa. Ƙasar ta ce ta kai ɗaruruwan hare-hare kan yankunan da Houthi ke iko da su, ciki har da Sanaa.

A ranar Litinin, gwamnatin Yemen ta ƙaddamar da wani farmaki kan Houthi. Daga bisani, ƙungiyar ta yi kira ga jiragen sama da su guji sararin samaniyar Saudiyya, tana mai ayyana shi a matsayin yankin ayyukan soji.

Houthi ta kuma yi gargaɗin cewa duk jirgin sama da ke shawagi a yankin zai iya zama abin kai wa hari, sai dai jiragen da ke kan biranen Makkah da Madina.

An kai hari a Saudiyya
Wani wuri na ci da wuta bayan kai hari a Saudiyya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Houthi sun kai hari Saudiyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa akalla mutane uku sun jikkata bayan hare-hare kan filayen jiragen sama na Jazan da Najran da ke kusa da iyakar Saudiyya da Yemen.

An kai hare-haren ne yayin da fada tsakanin Saudiyya da mayakan Houthi ke ƙara tsananta a kasar Yemen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng