Gargadin da Trump Ya Yi wa Amurkawa Bayan Mummunan Hari a Kasar Saudiyya
- Amurka ta gargaɗi ’yan ƙasarta da ke Saudiyya da su guji filin jirgin saman Sarki Khalid da kewaye bayan rahotannin hare-hare
- Ofishin jakadancin Amurka ya yi gargaɗin yiwuwar soke jirage da rufe sararin samaniya, tare da sanya takunkumin zirga-zirga
- Ya kuma shawarci Amurkawa su bi umarnin hukumomi, guji taruka da wuraren haɗari, tare da bibiyar sanarwar tsaro domin kare rayukansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Amurka ta buƙaci ’yan ƙasarta da ke Saudiyya da su guji filin jirgin saman Sarki Khalid da ke Riyadh da yankunan da ke kewaye.
Wannan gargadin ne a zuwa ne bayan rahotannin hare-hare kan filin jirgin Saudiyya wanda ya yi sanadiyar rayuka da dama.

Source: Getty Images
Saudiyya: Gargadin da Amurka ta yiwa Amurka
Gargadin na cikin wata sanarwar tsaro da Ofishin Jakadancin Amurka a Saudiyya ya fitar ranar Asabar, 10 ga Oktoba wanda ta wallafa a shafinta.
Sanarwar ta kuma yi gargaɗin yiwuwar soke jirage, rufe sararin samaniya da samun cikas ga zirga-zirgar matafiya.
“Ofishin Jakadancin Amurka ya samu labarin hare-haren da aka kai filin jirgin saman Sarki Khalid da ke Riyadh a ranar 10 ga Oktoba, kuma yana ba da shawarar ƙwarai ga dukkan ’yan ƙasar Amurka su guji filin jirgin da yankunan da ke kewaye."
Ya shawarci Amurkawa da su tabbatar da jadawalin tashin jiragensu kai tsaye ta hannun kamfanonin jiragen sama da filin jirgin, saboda yiwuwar samun cikas ga zirga-zirgar jiragen sama.

Source: Twitter
Takunkumi da sanya kan zarga-zirga
Ofishin ya kuma sanar da sanya takunkumin zirga-zirga ga ma’aikatan gwamnatin Amurka a ƙasar, inda ya bayyana cewa suna buƙatar izini na musamman kafin amfani da filin jirgin saman Sarki Khalid.
Ya ƙara da cewa ma’aikatan gwamnatin Amurka “ba a ba su izinin yin zirga-zirga a cikin tazarar mil 20 daga iyakar Yemen ba saboda haɗarin tsaro.”
A cewar sanarwar, ana kuma buƙatar izini na musamman kafin gudanar da tafiye-tafiyen aiki zuwa lardunan Jizan, Asir da Najran, da kuma biranen Qatif, Yanbu da Taif.
Duk da matsalolin tsaro, ofishin ya ce har yanzu ana ci gaba da bayar da hidimomin ofishin jakadanci ga ’yan ƙasar Amurka.
Ofishin ya buƙaci Amurkawa da su sake duba shawarwarin tafiye-tafiye na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka game da Saudiyya da Yemen, tare da yin rajista a shirin Smart Traveler Enrollment Program (STEP).
Ya bayyana cewa rajista a shirin na bai wa mutane damar samun sabbin bayanan tsaro, sannan yana sauƙaƙa wa ofisoshin jakadanci da na ƙasashen waje tuntuɓar ’yan ƙasar Amurka idan aka samu gaggawa.
Trump ya yi godiya ga Shugaba Putin
A baya, an ji cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya godewa Shugaban Rasha Vladimir Putin bayan sanar da cewa Rasha za ta gaggauta wadatar da Amurka da tan 300,000 na dizal.
Ma'aikatar Tsaron Amurka ta fitar da lasisin wucin gadi don karɓar dizal daga Rasha duk da takunkumin da aka kakaba mata.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya soki matakin, inda ya bayyana shi a matsayin "kyauta" ga Putin kuma ya faɗakar da cewa sauƙaƙa matsa lamba ba zai haifar da zaman lafiya ba.
Asali: Legit.ng

