Riyadh: An Kai Harin da Ya Girgiza Babban Birnin Saudiyya
- An ji fashe-fashe da dama a Riyadh ranar Alhamis yayin da ake ci gaba da faɗa tsakanin Saudiyya da mayakan Houthi na Yemen
- Houthis sun yi ikirarin cewa sun kai hari kan filin jirgin saman King Khalid da makami mai linzami, amma Saudiyya ba ta tabbatar da hakan ba
- A ranar Laraba, an kashe mutane uku tare da jikkata 36 a hare-haren da aka kai kan filayen jiragen saman Abha da Riyadh
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Riyadh - An ji fashe-fashe da dama a Riyadh, babban birnin Saudiyya, ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoban 2026.
An ji fashe-fashen ne yayin da ake ci gaba da yaƙi tsakanin Saudiyya da mayakan Houthi na Yemen.

Source: Twitter
Tashar France24 ta ce 'yan jaridar AFP da ke Riyadh sun ce sun ji karar fashe-fashen, yayin da ake ci gaba da gwabza yaƙi tsakanin Saudiyya da ƙungiyar Houthi a Yemen.

Kara karanta wannan
Mayakan Houthi sun kai hare haren da suka yi barna a filayen jiragen saman Saudiyya
Houthis sun yi ikirarin kai hari
A ranar Alhamis, Houthis sun ce sun kai hari kan filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na King Khalid da ke Riyadh, ta hanyar amfani da makami mai linzami.
Sai dai kawo lokacin wallafa wannan rahoton, babu wata sanarwa daga hukumomin Saudiyya da ta tabbatar da harin ko ta bayyana ko an samu asarar rayuka ko lalacewar kadarori.
Shaidu sun ce sun ji fashe-fashe da dama a sassa daban-daban na Riyadh.
An umurci jami'an diflomasiyya su fake
Rahotan Euronews ya ce an umurci jami’an diflomasiyya da ke ofisoshin jakadancin ƙasashensu a Riyadh da su zauna a cikin wuraren da suke, domin kauce wa duk wata barazana.
Haka kuma, an ce makarantun ƙasashen waje da ke babban birnin sun ɗauki matakan kariya sakamakon fashe-fashen.
An kashe mutane uku a hare-haren Laraba
Hare-haren na ranar Alhamis sun zo ne kwana guda bayan hukumomin Saudiyya sun ce an kashe mutane uku tare da jikkata wasu 36 a hare-haren da aka kai kan filayen jiragen saman ƙasa da ƙasa guda biyu.
Filayen jiragen saman da aka kai wa hari sun haɗa da Abha da King Khalid International Airport da ke Riyadh. Houthis, waɗanda Iran ke mara wa baya, sun ɗauki alhakin hare-haren.
Rahotanni sun ce wani hari da jirgin sama mara matuƙi ya kai kan filin jirgin King Khalid ranar Laraba ya yi sanadin mutuwar mutum guda, tare da haifar da tsaiko wajen jigilar jiragen sama har zuwa ranar Alhamis.
Hare-haren Houthis sun ƙaru
Ƙungiyar Houthi ta yi ikirarin kai hare-hare da dama kan Saudiyya a cikin 'yan kwanakin nan, yayin da rikicin Yemen ke ƙara tsananta.
Mayakan Houthi na samun goyon bayan Iran, yayin da Saudiyya ke mara wa gwamnatin Yemen ta ƙasa da ƙasa baya a rikicin da ya daɗe yana gudana.
A baya-bayan nan, Houthis sun kuma ɗauki alhakin wasu hare-hare da suka haɗa da harba makami mai linzami kan Riyadh.
Sai dai har zuwa lokacin da aka kammala rahoton, babu tabbacin da hukumomin Saudiyya suka bayar kan ikirarin sabon harin da Houthis suka ce sun kai kan filin jirgin King Khalid ranar Alhamis.

Source: Getty Images
An kai harin da ya shafi masallacin Annabi SAW

Kara karanta wannan
Ana jimamin hatsarin sojoji, fasinja ya mutu a jirgin da ke kan hanyar zuwa Legas
A wani labarin kuma, kun ji cewa an zargi mayakan Houthi da kai hari kan wata tashar rarraba wutar lantarki a birnin Madina da ke Saudiyya.
A cewar sanarwar da aka fitar, harin ya shafi tashar Taibah da ke samar da wutar lantarki ga Masallacin Annabi SAW.
Asali: Legit.ng
