Har Cikin Masallaci, Matashi ya Sharɓawa Sarkin Pawa Wuƙa a Wuya

Har Cikin Masallaci, Matashi ya Sharɓawa Sarkin Pawa Wuƙa a Wuya

  • Wani matashi ya bi Sarkin Pawa Abdullahi Ibrahim Ilali har cikin masallaci inda ya yi yunkurin masa yankan rago a Zaria
  • Matashin mai suna Umar ya lallaba har masallaci bayan sallar Asuba a ranar Juma'a da sharbebiyar wukarsa kuma tsirara babu kaya
  • Sai dai Allah bai baiwa Umar iko ba amma ya yanki Sarkin a wuya kafin a kai masa dauki tare da mika shi hannun hukuma

Zaria, Kaduna - Al'ummar Tudun Wadan Zaria sun tashi da alhini tare da tashin hankali a ranar Juma'a da ta gabata sakamakon yunkurin yi wa Sarkin Pawa yankan rago da wani matashi yayi har cikin masallaci.

Mummunan al'amarin ya faru ne da safiyar Juma'a yayin da Sarkin Pawa Abdullahi Ibrahim Ilali yake lazimi bayan kammala sallar asubahi ta ranar.

Kara karanta wannan

Abokin kirki: El-Rufa'i ya tuna yadda ya hadu da tsohon sarkin Kano Sanusi a jami'a

Legit.ng ta zanta da dan Sarkin, Sani A. Ibrahim

Kamar yadda Sani A. Ibrahim, da ga Sarkin Pawan ya zanta da Legit.ng, ya bada labari dalla-dalla na yadda matashi Umar yayi yunkurin mayar dasu marayu.

Sani ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da sanyin safiyar Juma'a da ta gabata ne muka shiga tsananin tashin hankali bayan wani matashi mai suna Umar yayi yunkurin mayar damu marayu.
Matashin ya je kofar masallacin da mahaifinmu yake sallah inda ya nade jikinsa da zani mai kama da hijabi yayin da yake tsirara babu kaya. Liman ne ya fara cin karo da shi bayan ya fito daga masallacin inda yace mishi ya shiga yayi sallah ko kuma idan bacci zai yi ya koma cikin masallacin.
Daga tashin matashi mai suna Umar, sai ya shiga masallacin inda ya tsaya kan mahaifinmu yayin da yake lazimi. Ya dube shi inda yace ya jira shi a kofar masallacin sanin cewa su kan kawo masa kara idan abu ya faru domin yayi sasanci.

Kara karanta wannan

Da gwamnati ta biya kudin fansata, ana sako ni zan yi murabus, Kwamishinan Niger

Mahaifinmu ya mayar da kai ya cigaba da lazimi, sai kawai ya ji an taba kanshi. Juyowar shi ke da wuya yaji wuka a kan makogwaronsa. Cike da sa'a mahaifinmu ya rike hannun Umar yayin da sauran wadanda ke masallacin suka taso domin kai mishi dauki.
An rike matashin tare da kokarin raba wukar daga wuyanshi yayin da Umar ke kokarin aiwatar da mummunan burin shi. A haka ne wukar ta yanke shi a wuya amma cikin ikon Allah bata shiga sosai ba. Take jini ya fara zuba yayin da Umar ya fara kokarin kaiwa jama'a yanka da wukar tare da yunkurin gudu.

Sani ya bada labarin yadda aka rike matashi Umar wanda bai wuce shekaru 25 ba tare da kokarin kwace wukar amma ya ki saki. Ya sanar da yadda aka karya hannunsa sannan ya saki wukar.

Tuni jama'a da 'yan uwa da suka taru suka fara dukan Umar amma Sarkin Pawa ya tsawatar tare da umartarsu da su mika matashin hannun hukuma.

Kara karanta wannan

Daga karshe, Hukumar Hizbah ta yi magana kan kayan da Zahra Bayero ta sanya

Babu bata lokaci aka tafi da Sarkin asibiti domin samun taimakon gaggawa na masana yayin da aka mika Umar hannun hukumar 'yan sanda a tsirarar shi.

Ko dai akwai wata jikakkiyar alaka tsakanin matashi Umar da Sarki?

Legit.ng ta so jin ko akwai alakar wani abu da ta taba hada Sarkin da matashin, sai Sani yace:

Tabbas alakar Ubangida da da ce ke tsakanin mahaifinmu da Umar. Shi ke kawo mana cefane gida kuma suna da alaka mai kyau da mahaifinmu. A takaice zan iya cewa shine kadai mutumin da zaka tambaya inda Sarki yake a kowanne lokaci kuma ya sanar da kai, babu shakka kaje zaka same shi. Kowa yayi mamakin yadda Umar ya iya yunkurin aiwatar da wannan mummunan nufi kan wanda ya rike shi kamar dan cikinsa.

Shin matashi Umar yana da tarihin tabuwar kwakwalwa ne?

Legit.ng ta tamabya domin jin cewa ko dai matashin yana da tabuwar kwakwalwa ne? Sani ya tabbatar da cewa bashi da tarihin tabin hankali, sai dai tabbas yana shaye-shaye.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Mutum 1 ya sheka lahira yayin da 'yan fashi suka kai farmaki bankuna 2

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel