Jerin sunaye: Jacob Zuma da sauran tsoffin shugabannin Afirka da aka daure kurkuku

Jerin sunaye: Jacob Zuma da sauran tsoffin shugabannin Afirka da aka daure kurkuku

A yayin da tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ya mika kansa ga ‘yan sanda don fara hukuncin daurin watanni 15 a gidan yari saboda raina kotu, Legit.ng a wannan rahoton ta kawo wasu manyan shugabannin Afirka da aka tura gidan yari.

An mika Zuma dan shekaru 79 a gidan yari a makon da ya gabata bayan ya ki halartar binciken cin hanci da rashawa.

KU KARANTA KUMA: Matar mutum kabarinsa: Matashi ya angwance da wata budurwa duk da nakasar da take da ita

Jerin sunayen: Jacob Zuma da sauran tsoffin shugabannin Afirka da aka daure kurkuku
Bayan daure Jacob Zuma a kurkuku, Legit.ng ta jero wasu manyan shugabannin Afirka da aka tura gidan yari Hoto: Garba Shehu
Asali: Facebook

1. Alphonse Massamba-Débat - Shugaban Kwango tsakanin 1963-1968

2. Ali Osman Taha - Mataimakin shugaban kasar Sudan tsakanin 2011-2013, 1998-2005

3. Baghdadi Mahmudi - Firayim Ministan Libya tsakanin 2006-2011

4. Ayaba, Kan'ana - Shugaban Zimbabwe tsakanin 1980–1987

5. Bokassa, Jean-Bédel - Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya -Sarki tsakanin 1976–1979 kuma shugaban kasa tsakanin 1966–1976

6. Carlos Correia - Firayim Ministan Guinea-Bissau tsakanin 2015-2016, 2008-2009, 1997-1998, 1991-1994

7. Chihana, Chakufwa - Mataimakin shugaban kasar Malawi tsakanin 2003-2004, 1994-1996

8. Diya, Oladipo - Mataimakin shugaban kasar Najeriya tsakanin 1993-1997

9. Ebeid, Atef - Firayim Ministan Masar tsakanin 1999-2004

10. Ephraïm Inoni - Firayim Ministan Kamaru tsakanin 2004-2009

11. Eugene Koffi Adoboli - Firayin ministan Togo tsakanin 1999-2000

12. Gregoire Kayibanda - Shugaban kasar Ruwanda tsakanin 1961-1973

13. Habib Bourguiba - Shugaban kasar Tunisia tsakanin 1957-1987 kuma Firayim Minista tsakanin 1956-1957

14. Haile Selassie - Sarkin Habasha tsakanin 1930-19194

15. Hama Amadou - Firayim Ministan Nijar tsakanin 2000-2007, 1995-1996

Tsohon shugaban kasar South Afrika ya mika kansa ga hukuma, ya shiga kurkuku

A gefe guda, mun ji cewa bisa biyyaya ga umurnin kotu, tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu, Jacob Zuma, ya mika kansa ga hukumar yan sanda domin jefashi cikin kurkuku na tsawon watanni 15.

Reuters ta ruwaito cewa Kakakin hukumar yan sanda, Lirandzu Themba, ya tabbatar da hakan a jawabin da ya saki ranar 7 ga Yuli, inda yace yanzu haka Zuma na hannunsu.

Kotu ta yanke hukuncin daure tsohon shugaba Zuma kan laifin kin amsa sammacin kotu kan zargin rashawa da ake masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel