Kotu ta ce za a kamo tsohon Shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma a Mayu
Wata Kotun kasar Afrika ta kudu ta bada iznin a cafke tsohon shugaba Jacob Zuma bayan ya ki halartar zaman shari’ar da ake yi domin a binciki zargin da ke wuyansa.
Jacob Zuma ya ki bayyana a gaban Alkali ne da uzurin cewa bai da lafiya. Sai dai yanzu Alkali ta yi watsi da uzurin, bada umarnin cewa a kamo mata tsohon shugaban.
Lauyan da ke kare Jacob Zuma a kotu ya fadawa Alkalin cewa bai da lafiya, inda ya mika wata takarda da ke nuna cewa ya na kwance a wani asibitin sojoji a kasar Cuba.
Alkali mai shari’a Dhaya Pillay, ba ta dauki wannan uzuri ba, ta fadawa Lauyan wanda ake zargi cewa babu wata hujja da za ta nuna gaskiyar takardar da ya gabatar a kotu.
“Ban sani ba ko … Likita. Babu … abin da ya ke nuna cewa Likita ne (ya rubuta wannan).” Inji Alkalin shari’ar, a lokacin da ta ke shirin bada iznin cafke tsohon shugaban.
KU KARANTA: Duk da kashe-kashe Najeriya ta fi ko ina zaman lafiya Inji Minista
A zaman da aka yi a makon nan, babban mai kare wanda ake tuhuma, Lauya Dan Mantsha, bai iya gamsar da kotu cewa Jacob Zuma ya na kwance a asibiti a kasar Cuba ba.
Ana zargin Jacob Zuma da laifuffuka 18 wadanda su ka kunshi satar kudi, almundahana, da badakalar kudin makamai tun a lokacin ya na mataimakin shugaban kasa.
Mai shari’ar ta bayyana cewa takardar da aka gabatar ba za ta daukewa Zuma halartar shari’a ba, don haka ta bukaci ya kawo kansa da kansa a gaban kotu, ko a kamo shi.
Alkalin ta ba Zuma daga yanzu zuwa Ranar 6 ga Watan Mayu domin ya hallara a kotu. Da zarar wa’adin ya wuce, za a ba jami’an tsaro damar su cafke shi da karfi da yaji.
Akwai zargin satar kudi a kan Zuma wanda ya yi mulki daga 2009 zuwa 2018, kafin ya yi murabus. A Najeriya kuma, Shugaba Buhari ya ba Daniel Amokachi mukami.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng