Yadda Rasha ke Taimakon Iran Wajen Hada Makamai Masu Linzami
- Rahotanni sun ce gwamnatin kasar Rasha na taimakawa Iran a sirrance wajen haɓaka fasahar makamai masu linzami masu saurin kai farmaki
- Shirin, mai lambar sirri C430L, ya fara ne a shekarar 2023, inda ake zargin kamfanin fitar da makaman Rasha na Rosoboronexport ne ya shirya shi
- Masana sun ce fasahar da ake haɓakawa za ta iya bai wa Iran damar amfani da makaman wajen kai hare-haren jiragen ruwa da kuma wuraren da ke kan tudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Moscow – Rasha na taimakawa Iran a ɓoye wajen haɓaka fasahar makamai masu linzami masu saurin wuce sautin dan Adam, kamar yadda a rahoto ya nuna a ranar Laraba.
Rahoton ya ce shirin na iya samar da makamai masu linzami da za a iya amfani da su wajen kai hare-haren jiragen ruwa da kuma wuraren da ke kan tudu.

Kara karanta wannan
Lauya ya tsage gaskiya, an ji dalilin da ya sa Amurka ba ta kama Shugaba Tinubu ba

Source: Getty Images
Rasha na taimakon Iran tun 2023
A cewar Jerussalem Post, shirin mai lambar sirri C430L ya fara ne a shekarar 2023, kuma kamfanin Rosoboronexport mai kula da fitar da makaman Rasha ne ya shirya shi tare da haɗin gwiwar NPO Mashinostroyenia, wanda Amurka ta kakaba wa takunkumi.
Rahoton ya ce jami’an fitar da makamai na Rasha da manyan injiniyoyin NPO Mashinostroyenia sun yi tafiye-tafiye zuwa Iran sau da dama a shekarar 2023 domin gudanar da aikin.
Daga cikin injiniyoyin da suka je Iran akwai Alexander Dergachev, babban mai tsara makamai masu linzami da ake harbawa daga teku da tsarin makamai masu linzami masu cin dogon zango.
Haka kuma akwai Alexander Chebakov, shugaban sashen ƙira na NPO Mashinostroyenia da ke kula da na’urorin motsa makamai, da Yuri Prokhorchuk, shugaban sashen binciken yanayin motsin iska.

Source: Getty Images
Jami’in Rasha da ya shiga aikin
Financial Times ta ce Vladislav Kuzmichev, shugaban sashen fasahar tsaro da sararin samaniya na Rosoboronexport, ya raka tawagar Rasha a ziyararta ta uku zuwa Iran.
Rahoton ya ce daga baya Kuzmichev ya shiga tattaunawar yarjejeniyar C430L da Iran.
Ya zuwa shekarar 2025, NPO Mashinostroyenia ta samu wasu takardun fasaha daga Iran, inda injiniyoyin Rasha suka gudanar da bincike a kansu tare da mayar da martani kan tambayoyin da suka taso.
A cikin wasiƙun da aka gani na watan Afrilun 2025, Rosoboronexport ta gabatar da shawarar tura wata tawagar ƙwararrun Rasha zuwa Iran.
Kamfanin ya kuma nemi Tehran ta amsa tambayoyin injiniyoyin kafin tawagar ta sake zuwa ƙasar.
Pezeshkian ya gode wa Putin
A wani labarin mun ruwaito cewa Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya gode wa Shugaban Rasha, Vladimir Putin, kan matsayin Moscow game da yaƙin Iran da takunkuman da suka biyo baya.
Pezeshkian ya ce Iran da Rasha za su iya haɗa kai wajen tinkarar abin da ya kira “son zuciyar Amurka na tafiyar da harkokin duniya ita kaɗai”.
Shugabannin biyu sun gana ne a gefen taron SCO a Bishkek, babban birnin Kyrgyzstan, inda Putin ya tabbatar da cewa Rasha za ta ci gaba da goyon bayan al’ummar Iran.
Asali: Legit.ng
