Iran Ta Fadi Abin da ba Za Ta Taɓa Mantawa ba, kuma ba Za Ta Yafe wa Amurka ba
- Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Iran ba za ta taɓa mantawa ko yafe harin makarantar Minab ba
- Araghchi ya bayyana ɗaliban da aka kashe a harin a matsayin “jarumai” ga Iran, yayin da ake ci gaba da tunawa da su
- Mahukuntan Iran sun zargi Amurka da kai harin, yayin da Washington da Isra’ila ba su amince da alhakin kai harin ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya yi magana game da harin da Amurka ta kai a makaranta wanda ya kashe yara dalibai.
Araghchi ya ce ƙasarsa ba za ta taɓa “mantawa” ko “yafe” mummunan harin da aka kai makarantar Minab ba wanda ya yi ajalin yara dalibai.

Source: Getty Images
Araghchi ya bayyana hakan ne yayin da ya ziyarci wani baje kolin fasaha a Tehran, wanda aka shirya domin girmama ɗalibai da sauran mutanen da suka rasa rayukansu, cewar Al Jazeera.
Iran ta tuna daliban da Amurka ta kashe
Ministan ya bayyana ɗaliban da aka kashe a harin a matsayin “jaruman alama” ga Iran, yana mai cewa tunaninsu zai ci gaba da kasancewa cikin zukatan al’ummar ƙasar.
Wannan magana ta zo ne watanni bayan mummunan harin da aka kai makarantar Shajareh Tayyebeh da ke Minab, a kudancin Iran.
Mahukuntan Iran sun zargi Amurka da alhakin kai harin, yayin da Amurka da Isra’ila ba su fito fili sun amince da cewa su ne suka kai harin ba.
Kungiyoyin kare hakkin ɗan Adam na duniya sun yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa domin gano gaskiyar abin da ya faru.
Harin ya faru ne a ranar 28 ga Fabrairu, a lokacin da aka fara wani gagarumin farmakin soji da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran.
Mahukuntan Iran sun ce mafi yawan wadanda harin ya rutsa da su yara ne ‘yan makaranta, lamarin da ya sanya harin cikin mafi muni a lokacin rikicin.
An shirya baje kolin fasahar a Tehran a matsayin wurin tunawa da wadanda aka kashe, inda zane-zane ke nuna rayuwarsu tare da adana tarihinsu.
Kalaman Araghchi sun nuna cewa harin na ci gaba da kasancewa muhimmin batu na siyasa da kuma abin da ke tayar da hankali a Iran.
Jami’an Iran sun sha neman a hukunta wadanda suka aikata harin, tare da bayyana lamarin a matsayin babban take hakkin dokokin kasa da kasa.
Illar da yakin Iran ya yi wa Amurka
Mun ba ku labarin cewa Amurka na fuskantar ƙarancin makamai masu linzami na Patriot a Turai, yayin da yaƙin Iran ya sa aka tura da dama Gabas ta Tsakiya.
Jami’an tsaro sun ce ƙarancin Patriots na iya rage ikon NATO na kare ƙasashen Turai daga hare-haren makamai masu linzami na Rasha.
Sai dai NATO da Pentagon sun musanta cewa ƙarancin makaman ya kai matakin damuwa, suna cewa suna da isassun makamai domin kare ƙasashe da bukatun Amurka.
Asali: Legit.ng

