Ana cikin Yaki da Amurka, Saudiyya ta kai hare hare 40 kan Kawayen kasar Musulunci Ta Iran
- Rahotanni sun ce jiragen yaƙin Saudiyya sun kai hare-haren sama kusan 40 kan wasu gundumomi a Taiz, lardin Hodeidah, Al-Jawf da Marib
- Kafofin yaɗa labaran Yemen sun ruwaito hare-hare a yankunan As-Salif da At-Tuhayta da kuma tsibirin Kamaran
- Jakadan Yemen a Qatar ya zargi Iran da kitsa sabon faɗan da ya ɓarke a ƙasar, yana mai cewa tana amfani da Houthis wajen ƙara ƙarfafa ikonta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Saudi Arabia - Jiragen yaƙin Saudiyya sun kai hare-haren sama kusan 40 kan wasu yankunan a Taiz, lardin Hodeidah, Al-Jawf da Marib da ke kasar Yamen.
Kamfanin dillancin labarai na Saba, wanda Houthis ke iko da shi, ya ce an kai hare-hare a gundumomin As-Salif da At-Tuhayta, da kuma tsibirin Kamaran da ke Yemen.

Source: Getty Images
Haka kuma tashar TRT World ta ruwaito cewa an kai hare-haren sama 18 a gundumomin Al-Hazm, Al-Ghayl da Al-Jubah.
Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, rundunar haɗin gwiwar da Saudiyya ke jagoranta a Yemen ba ta tabbatar da hare-haren ba.
Me ya sake dawo da fadan Yemen?
Jakadan Yemen a Qatar, Rajeh Badi, ya ce Iran ce ke bayan sabon faɗan da ya sake ɓarkewa a ƙasar, kuma tana amfani da Houthi wajen ƙara ƙarfafa ikonta kan hanyoyin jigilar kayayyaki a Bahar Maliya.
Da yake magana da tashar Al Jazeera, Badi ya zargi kungiyar Houthis da fara sabon faɗan.
Ya ce abin da ke faruwa a yanzu “farmakin bazata ne na Houthi da nufin ƙwace muhimman wurare a gabar Bahar Maliya”, wanda ake son amfani da shi wajen taimaka wa Tehran wajen samun iko kan hanyoyin ruwa.
Ana zargin Iran ta tada yakin Yemen
Badi ya ce alaƙar Iran da Houthis “ba wani sirri ba ce”, yana mai bayyana ƙungiyar a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin da Iran ke amfani da su a yankin, tare da Hezbollah a Lebanon da PMF a Iraq.

Kara karanta wannan
Ana tsaka da yakin Iran, ƙasar Saudiyya ta kai munanan hare hare kan manyan birane 3
Ya ce yayin da sauran ƙawayen Iran ke fuskantar matsin lamba, Tehran na “ƙara dogaro da Houthis a matsayin ragowar damar da take da ita”, kuma ta taimaka wajen sake kunna yaƙin bayan an samu kusan shekara biyar ana samun sassauci.

Source: Getty Images
Gargadin kan mashigar ruwa
Badi ya tuna da marigayi tsohon shugaban Yemen, Abd-Rabbu Mansour Hadi, wanda ya taɓa cewa idan Iran ta mallaki mashigar Bab al-Mandeb da mashigar Hormuz, “ba za ta buƙaci makamin nukiliya ba”.
“Ƙarfafa ikonta kan waɗannan mashigai guda biyu zai fi ƙarfin duk wani tarin makaman nukiliya,” in ji Badi. “Abubuwan da suka faru sun tabbatar da cewa ya yi gaskiya.”
Najeriya ta yi tir harin Houthi a Saudiyya
Kun ji cewa Gwamnatin Najeriya ta yi Allah-wadai da sabon harin Houthis kan Saudi Arabia, wanda ya jikkata mutane 73 tare da lalata wata cibiyar mai.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta ce sabon rikicin barazana ne ga zaman lafiyar yankin da samar da makamashi a duniya.
Najeriya ta bayyana sabbin tashe-tashen hankulan a matsayin babbar barazana, sannan ta bukaci bangarorin da ke fada su mutunta dokokin kasa da kasa.
Asali: Legit.ng
