Iran Ta Nuna Jan Wuya, Ta Kama Jirgin Ruwan da Trump Ya Tura Hormuz
- Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ta ce ta kama wani jirgin ƙarƙashin ruwa mara matuƙi na Amurka a ƙofar Mashigar Hormuz
- Kafafen yaɗa labaran Iran sun ce jirgin samfurin Dive-LD ne, wanda kamfanin tsaro na Anduril da ke California ya ƙera domin ayyukan soji
- Sai dai Ma'aikatar Tsaron Amurka ta ce jirgin ya samu matsala fiye da kwana guda da ya wuce, tana mai cewa ba ya ɗauke da muhimman bayanai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Tehran – Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ta ce ta kama wani jirgin ƙarƙashin ruwa mara matuƙi na Amurka a ƙofar Mashigar Hormuz.
Lamarin ya ba da wani sabon haske kan yadda ake amfani da jiragen ƙarƙashin ruwa marasa matuƙa wajen gudanar da ayyukan soji da tattara bayanai.

Source: Getty Images
Reuters ta rahoto cewa kafafen yaɗa labaran gwamnatin Iran sun bayyana jirgin a matsayin Dive-LD, wani babban jirgin ƙarƙashin ruwa mai cin gashin kansa da kamfanin tsaro na Anduril da ke California ya ƙera.
Yadda Iran ta kama jirgin Amurka
Rundunar sojin ruwa ta Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ta ce ta kama jirgin ne a ƙofar Mashigar Hormuz.
Ta bayyana cewa jirgin na ɗaya daga cikin jiragen ƙarƙashin ruwa marasa matuƙi masu fasaha a rundunar sojin Amurka.
A cikin wata sanarwa da kafafen yaɗa labaran Iran suka wallafa, rundunar ta ce:
“Mun kama ɗaya daga cikin jiragen ƙarƙashin ruwa mafi girma na sojojin Amurka a ƙofar Mashigar Hormuz. Wannan jirgin yana ɗauke da sababbin fasahohi.”
Aikin da jirgin ke yi
Jirgin Dive-LD yana da tsawon ƙafa 19, wato kusan mita 5.8, kuma an ƙera shi domin gudanar da ayyuka daban-daban a ƙarƙashin ruwa.
Daga cikin ayyukan da yake iya gudanarwa akwai ganowa da kawar da nakiyoyi, taswirar ƙarƙashin teku, tattara bayanan sirri da kuma duba gine-ginen da ke ƙarƙashin ruwa kamar igiyoyin sadarwa da bututun mai.
Rahoton New York Post ya nuna cewa kamfanin Anduril ya ce jirgin na iya yin aiki har na tsawon kwanaki 10 ba tare da komawa sansaninsa ba.
Haka kuma an ƙera shi tare da ba shi damar nutsewa zuwa zurfin da ya kai mita 6,000, wato kusan ƙafa 19,700.

Source: Facebook
A nasa martanin, wani kakakin ma'aikatar yakin Amurka, Pentagon, ya ce wani jirgin ƙarƙashin ruwa mara matuƙi ya samu matsala fiye da kwana guda kafin sanarwar Iran.
Houthi sun kai hari Saudi
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan tawayen Houthi da Iran ke marawa baya a Yemen sun ƙaddamar da wani gagarumin hari a kudu maso yammacin Saudiyya da safiyar Talata.
Hare-haren sun shafi wuraren samar da mai da sauran muhimman abubuwan more rayuwa, lamarin da ya ƙara fargabar faɗaɗa rikice-rikicen yankin tare da ƙara matsin lamba kan farashin ɗanyen mai.
Dakarun da Saudiyya ke jagoranta sun yi alƙawarin mayar da martani mai ƙarfi, yayin da Ma'aikatar Makamashin ƙasar ta ce hare-haren sun haifar da gobara a wasu cibiyoyi a kudancin ƙasar.
Asali: Legit.ng

