DSS Ta Yi Magana kan Zargin Sanata da Taimakon 'Yan Ta'adda
- Sanata Shehu Buba mai wakiltar mazabar Bauchi ta Kudu a majalisar dattawa na fuskantar sabbin zarge-zargen tallafa wa ’yan bindiga
- Buba, wanda ke wakiltar mazabar Sanatan Bauchi ta Kudu, ya dade yana musanta zarge-zargen alakarsa da ’yan bindiga a Najeriya
- Sababbin zarge-zargen sun fito ne daga wani mazaunin yankin da aka bayyana da sunan Hassan, wanda ya yi ikirarin a kan Sanata Shehu Buba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi – Tsohon shugaban kwamitin Majalisar Dattawa kan Tsaron Kasa da Leken Asiri, Sanata Shehu Buba, na sake fuskantar zarge-zargen alakarsa da ’yan bindiga yayin da yake kokarin wanke kansa daga zargin.
Shehu Buba, wanda ke wakiltar mazabar Sanatan Bauchi ta Kudu, ya fuskanci irin wadannan zarge-zarge tun shekarar 2024, amma ya ci gaba da musanta cewa yana da alaka da ’yan bindiga.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa wani mai suna Hassan ya yi sabon zargin ne yayin wata hira da wani mai tasiri a kafafen sada zumunta, D English Alhaji Media, inda ya ce wasu ’yan siyasa na taimaka wa ’yan bindiga a yankin.
Zargin da aka yi wa Shehu Buba
Hassan ya kuma yi ikirarin cewa wasu mutanen da ke da alaka da fitaccen shugaban ’yan bindiga, Dogo Gide, an kawo su Abuja domin horas da su.
Ya yi zargin cewa wani mataimaki ko na kusa da Sanata Shehu Buba ne ya taimaka wajen gudanar da wannan horo.
Sai dai Buba ya musanta zargin, inda a wata hira da aka wallafa a Bauchi ranar Alhamis, ya ce wasu ’yan siyasa ne ke daukar nauyin Hassan domin bata masa suna.

Source: Original
Sanatan ya ce ya riga ya gabatar da korafi a hukumance ga Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, inda ya kara da cewa an kama mutane hudu da ake sa ran gurfanar da su a kotu nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan
Dan Majalisa ya kai ƙorafi gaban shugaban Amurka kan abin da ake wa Tinubu a Najeriya
Bayanin hukumar DSS
A nata bangaren, wani kakakin DSS ya shaida cewa za a wallafa binciken zarge-zargen da ake yi kan sanatan a lokacin da ya dace.
Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan zarge-zargen da ake yi wa sanatan a sakon da ya wallafa a Facebook.
Dalung ya ce ya kamata DSS ta fayyace matsayin bincikenta, yayin da ya bukaci Majalisar Dokoki ta kasa ta yi la’akari da gudanar da nata binciken saboda tsohon mukamin da Buba ya rike wanda ya shafi harkokin tsaro da leken asiri na kasa.
Fintiri ya wanke Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, ya bukaci shugabannin Arewa su dauki alhakin rashin tsaron da ke addabar yankin tare da neman mafita mai dorewa maimakon daura laifi kan Bola Tinubu.
Fintiri ya yi wannan kira ne ranar Alhamis yayin wani taron masu ruwa da tsaki na APC a Yola, inda ya soki dabi’ar wasu ’yan Arewa na daura wa shugabannin Kudu alhakin matsalolin tsaro.
Ya tuna cewa a zamanin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, an zarge shi da haifar da yanayin da ya kai ga bullar Boko Haram, yana mai cewa ’yan ta’addan sun fito ne daga yankin.
Asali: Legit.ng
