Bayan Dawowa Yakin Iran, Kim Jong Un Ya Gargadi Trump kan Makamin Nukiliya
- Koriya ta Arewa ta ce har yanzu Amurka na ci gaba da nuna mata ƙiyayya, tare da yin alkawarin ƙara ƙarfafa makamanta na nukiliya
- Ƙasar ta yi watsi da kiraye-kirayen Amurka na ganin ta yi watsi da makamanta na nukiliya, tana mai cewa makaman na da muhimmanci a gare ta
- Koriya ta Arewa ta kuma soki atisayen soji da Amurka, Koriya ta Kudu da Japan ke shirin gudanarwa, tana mai cewa ba za ta yarda ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Pyongyang – Koriya ta Arewa ta ce manufar Amurka ta nuna ƙiyayya a kanta ba ta sauya ba, yayin da ta sha alwashin ci gaba da ƙarfafa makamanta na nukiliya tare da yin watsi da kiraye-kirayen Washington na rusa su.
Rahoto ya nuna cewa ma’aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da kafar yada labaran ƙasar, KCNA, ta wallafa ranar Litinin.

Source: Getty Images
Koriya ta Arewa ta soki Amurka
Rahoton Reuters ya nuna cewa kakakin ma’aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa ya zargi gwamnatin Amurka da ci gaba da ɗaukar matakin adawa da Pyongyang ta hanyar dagewa kan buƙatar “cikakken kawar da makaman nukiliya.”
Ya kuma soki yadda Washington ke sukar tarihin kare haƙƙin bil’adama na Koriya ta Arewa da kuma shirye-shiryen gudanar da atisayen soji tare da Koriya ta Kudu da Japan.
Kakakin ya ce gwamnatin Shugaba Donald Trump ta sake tabbatar da manufarta ta ƙiyayya, wadda take neman, a cewarsa, keta ’yanci, tsarin siyasa da muradun tsaron Koriya ta Arewa.
Batun makamin nukiliya
Kakakin ya bayyana makaman nukiliya na Koriya ta Arewa a matsayin “tabbatacciyar kariya” da ke tabbatar da ikon mallakar ƙasar da kuma tsaronta.
Ya ce matsayin Koriya ta Arewa na kasancewa ƙasar da ke da makaman nukiliya ba zai sauya ba saboda yawan kiraye-kirayen da Amurka ke yi na neman ta kawar da makamanta.
The Economic Times ta wallafa cewa ya kuma ce tsammanin rage tashin hankali a yankin ba shi da amfani, yana mai jaddada cewa babu wani sauyi a manufar ƙasar dangane da Amurka.

Source: Getty Images
Sanarwar Koriya ta Arewa ta zo ne bayan Shugaba Donald Trump ya bayar da umarnin rage girman atisayen sojin Ulchi Freedom Shield da ake gudanarwa duk shekara tsakanin Amurka da Koriya ta Kudu.
Iran ta kai hari kan Amurka
A wani labarin, mun ruwaito cewa Iran ta ce ta harba makamai masu linzami kan sansanonin sojin Amurka guda biyu da ke Jordan, a matsayin ramuwar gayya kan wani hari da Amurka ta kai wa tsibirin Larak da ke Kudancin Iran.
Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta ce hare-haren makami mai linzami da jirage marasa matuka da ta kira Martani ga azzalumai' sun shafi sansanonin King Hussein da Al Azraq a Jordan.
Jordan ta ce tsarin kariyar sararin samaniyarta ya tare makamai masu linzami guda takwas da suka kutsa cikin sararin samaniyar ƙasar da sanyin safiyar Litinin.
Asali: Legit.ng

