Wata Sabuwa: Trump Ya Yi Abin da Zai Sake Fusata Iran yayin da Ake Musayar Wuta
- Donald Trump ya ba da shawarar sauya sunan mashigar Hormuz zuwa “Trump Strait”, yana mai cewa yanzu Amurka ce ke da cikakken iko a mashigar
- Fadar White House ta wallafa taswirar mashigar tare da sabon sunan da Trump ya bayar, yayin da ake ci gaba da yaki
- Trump ya sha yin sauye-sauyen sunayen wurare, ciki har da sauya “Gulf of Mexico” zuwa “Gulf of America” da kuma “Lake Ontario” zuwa “Lake America”
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Washington, D.C. - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ba da shawarar sauya sunan mashigin Hormuz zuwa “Trump Strait”,
Kalaman Trump na zuwa ne duk da cewa ana ci gaba da samun arangama tsakanin Amurka da Iran a yankin Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
Trump ya yi wannan magana ne a ranar Laraba, 2 ga watan Satumban 2026 a shafinsa na Truth Social.
Shugaba Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake ikirarin cewa Amurka ta samu cikakken iko kan mashigar Hormuz, wata muhimmiyar hanyar ruwa da ke tsakanin Tekun Farisa da Tekun Oman.
A wani rubutu da ya wallafa, Trump ya ce:
“Yanzu da muka mallake shi a ƙarƙashin ikon Amurka, ya kamata mu sauya sunan mashigar Hormuz zuwa Trump Strait?”
Ya ƙara da cewa, kamar yadda Amurka take, sabon sunan zai kasance “mai zafi fiye da kowane lokaci”.
Fadar White House ta goyi bayan shawarar
Bayan Trump ya yi wannan magana, Fadar White House ta wallafa wata taswirar yankin Gulf a kafafen sada zumunta.
Taswirar ta nuna sunan “Trump Strait” a matsayin sabon sunan mashigar Hormuz.
A cikin makonnin baya-bayan nan, Trump ya sha yin barazanar cewa Amurka za ta mallaki mashigar Hormuz, har ma ya wallafa wata taswira da ta nuna mashigar a matsayin sabon yanki na Amurka.
Donald Trump ya ce ba da gaske yake nufi ba
Sai dai daga baya Trump ya rage muhimmancin maganar, yana mai cewa bai tabbatar da cewa za a sauya sunan mashigar ba.
The Punch ta ce bayan wani ɗan jaridar AFP ya tambaye shi a Ofishin Oval ko da gaske yake nufin sauya sunan mashigin Hormuz, Trump ya amsa cikin dariya cewa: “An dai yi maganar ne kawai.
Duk da haka, wasu daga cikin shawarwarin Trump na baya da aka fara ɗauka a matsayin barkwanci sun kasance suna tabbata daga baya.
Trump ya sauya wasu sunaye
A makon da ya gabata, Trump ya sanya hannu kan umarnin sauya sunan Lake Ontario zuwa “Lake America”, a daidai lokacin da rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da Kanada ya tsananta.
Hakan ya faru ne kwanaki kaɗan bayan da Trump ya fara bayyana wannan ra’ayi cikin yanayin barkwanci.
A watan Janairun 2025, a ranar farko da ya koma Fadar White House, Trump ya kuma sauya sunan Gulf of Mexico zuwa “Gulf of America”. Sai dai Mexico da Kanada ba su amince da waɗannan sauye-sauyen sunaye ba.

Source: Getty Images
An kai karar Amurka kan hari a Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa Ƙungiyar Red Crescent ta Iran ta buƙaci kotun ICC ta ɗauki matakin shari’a tare da bincikar harin makami mai linzami da Amurka ta kai.
Kungiyar ta aika wa ICC wasiƙa inda ta ce kasancewar wurin da aka kai harin a matsayin wajen gudanar da bikin aure.
Asali: Legit.ng


