An Ce Sojojin Amurka Sun Tonawa Trump Asiri kan Yakin Iran, ana Bincike

An Ce Sojojin Amurka Sun Tonawa Trump Asiri kan Yakin Iran, ana Bincike

  • Kimanin jami’an sojan Amurka 50 na fuskantar bincike kan zargin fitar da bayanan sirri ga manema labarai game da yaƙin da ƙasar ke yi da Iran
  • Rahotanni sun ce binciken ya mayar da hankali kan yadda wasu muhimman makaman Amurka ke raguwa, ciki har da makamai masu linzami
  • An kuma yi wa wasu jami’an soja da ma’aikatan farar hula gwajin gano ƙarya domin gano ko sun fallasa bayanan sirri ga ’yan jarida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington – Amurka na gudanar da bincike kan kusan jami’an soja 50 da ake zargin sun fitar da bayanan sirri ga manema labarai game da yaƙin Iran, musamman bayanan da suka shafi raguwar tarin muhimman makamai.

Rahotanni daga kafafen yada labaran Amurka sun ce jami’an rundunar Joint Chiefs of Staff na daga cikin wadanda aka yi wa gwajin gano ƙarya a watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun fatmaki mutane ana shirin yin sallah, an rasa rayukan bayin Allah

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump a wajen taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

New York Times ta ruwaito cewa binciken ya biyo bayan rahotannin manema labarai da suka bayyana karancin wasu muhimman makamai, ciki har da makamai masu linzami masu dogon zango da makamai masu kariya na Patriot.

An yi gwajin ga sojoji

Rahotannin sun ce an yi wa jami’an soja da ma’aikatan farar hula gwaji domin gano ko sun bai wa ’yan jarida bayanan sirri da suka shafi raguwar tarin makaman Amurka.

An ce bayanan da aka fitar sun hada da matsalar raguwar wasu manyan makamai da ake amfani da su a ayyukan soji.

Al Jazeera ta ruwaito cewa an kuma yi wa wasu jami’ai da dama gwajin, ciki har da jami’an CENTCOM da sauran rundunonin soji da ke gudanar da ayyuka a wurare daban-daban.

Shugaba Donald Trump
Donald Trump yayin wani jawabi ga Amurkawa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Adadin sojojin da aka gwada

Ana amfani da gwajin ne lokaci-lokaci wajen sake tabbatar da izinin tsaro na jami’an da ke da damar samun bayanan sirri da ake boyewa ko shirye-shiryen sirri na musamman.

Kara karanta wannan

Daliban ABU Zaria sun kera na'urar da makafi za su rika tafiya da ita cikin salama

Sai dai wasu jami’ai sun shaida cewa yawan mutanen da aka yi wa gwajin a wannan bincike ya kasance abin da ba a saba gani ba.

Rahotannin kafafen yada labaran Amurka sun ce binciken ya fi karkata ne kan bayanan da suka bayyana cewa tarin wasu manyan makamai na Amurka na raguwa.

Hukumomin Amurka na kokarin gano ko jami’an soja ko ma’aikatan gwamnati ne suka bai wa manema labarai bayanan da ba a yarda a bayyana wa jama’a ba.

Trump ya zargi 'yan Democrat

A wani labarin, mun ruwaito cewa Donald Trump ya zargi ’yan jam’iyyar Democrat da sauran abokan hamayyarsa da fatan Amurka ta sha kashi a yaƙin Iran.

Trump ya sanar da cewa ’yan Democrat da ’yan Kwaminisanci sun fi son Amurka ta sha kashi a yaƙin Iran fiye da ya yi nasara a fagen daga

Ya kuma bayyana abokan hamayyarsa a matsayin “mutane marasa lafiya sosai”, yana mai amfani da wasu kalmomi marasa dadi ga 'yan adawan kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng