Amurka Ta Kashe Masu Bikin Aure a Iran, ana Son Maka Trump a Kotun ICC
- Ƙungiyar Red Crescent ta Iran ta buƙaci kotun ICC ta gudanar da bincike kan harin makami mai linzami da Amurka ta kai wajen biki
- Ƙungiyar ta ce harin da aka kai kan wurin da fararen hula ke gudanar da bikin aure ya kashe mutane huɗu tare da jikkata wasu 67
- Red Crescent ta ce harin na iya zama laifin yaƙi, kuma ya kamata a gudanar da bincike mai zaman kansa, ba tare da son rai ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Tehran – Ƙungiyar Red Crescent ta Iran ta buƙaci kotun ICC ta ɗauki matakin shari’a tare da bincikar harin makami mai linzami da Amurka ta kai kan wani bikin aure a Kuhestak, jihar Hormozgan.
Ƙungiyar ta aika wa ICC wasiƙa inda ta ce kasancewar wurin da aka kai harin a matsayin wajen gudanar da bikin aure da kuma kasancewar fararen hula a wurin ya haifar da babbar damuwa game da dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa.

Source: Getty Images
Red Crescent ta nemi bincike
Ƙungiyar ta wallafa a X cewa lamarin na buƙatar gudanar da bincike mai zaman kansa, adalci, cikakke kuma mai inganci domin gano abin da ya faru.
Ta ce:
“Saboda rahotannin da ke nuna cewa wurin da aka kai harin wajen bikin aure ne, tare da kasancewar fararen hula a wurin, lamarin na haifar da babbar damuwa ƙarƙashin dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa kuma ya cancanci bincike mai zaman kansa, ba tare da son rai ba, cikakke kuma mai inganci.”
Ta kuma bayyana cewa kai hari da gangan tare da sanin cewa hakan zai haifar da mutuwar fararen hula ko jikkata su na iya zama laifi ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa.
Harin ya kashe mutane huɗu
Al Jazeera ta wallafa cewa Red Crescent ta ce harin da aka kai kan bikin auren ya kashe mutane huɗu tare da jikkata wasu 67.
Ƙungiyar ta ce irin wannan hari na iya zama laifin yaƙi, tana mai buƙatar ICC ta gudanar da bincike domin tantance alhakin waɗanda suka kai harin.
Iran ta ce an kai hari kan wurin fararen hula ne, yayin da Amurka ta ce ba ta taɓa kai hari kan fararen hula da gangan ba.

Source: Facebook
Ana cikin haka ne kuma rundunar IRGC ta ce wasu tankokin dakon mai biyu sun taka nakiyoyin ruwa tare da lalacewa yayin da suke ƙoƙarin ratsa mashigar Hormuz.
Rasha na taimaka wa Iran
A wani labarin, mun ruwaito cewa Rasha na taimakawa Iran a sirrance wajen haɓaka fasahar makamai masu linzami masu saurin wuce sautin ɗan Adam, kamar yadda wani bincike ya bayyana.
Rahoton ya ce shirin mai lambar sirri C430L ya fara ne a shekarar 2023, inda kamfanin fitar da makamai na Rasha, Rosoboronexport, ya shirya shi tare da haɗin gwiwar NPO Mashinostroyenia.
A cewar rahoton, ƙwararrun injiniyoyin makamai na Rasha sun riƙa zuwa Iran domin taimakawa wajen haɓaka fasahar da za ta bai wa makamai masu linzami damar yin tafiya da saurin gaske.
Asali: Legit.ng

