Babbar Magana: Trump Ya Kawo Dokar da Ta Shafi Kasahen duniya baki daya
- Gwamnatin Amurka ta dakatar da bayar da bizar shige da fice a fadin duniya yayin da gwamnatin Donald Trump ke kara tsaurara dokoki
- Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce an soke wani shirin da aka riga aka tsara domin bai wa jami'an ofisoshin jakadanci karin horo
- Matakin na da nufin tabbatar da cewa masu neman bizar ba za su dogara da tallafin gama gari na gwamnatin Amurka ba bayan shiga kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka – Gwamnatin Amurka ta dakatar da ba da bizar shige da fice a dukkan kasashen duniya yayin da gwamnatin shugaban kasa Donald Trump ke kara tsaurara matakan kula da masu neman shiga kasar.
Wani jami'in Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ya tabbatar da matakin ranar Talata, inda ya ce an fara aiwatar da tsarin a dukkan ofisoshin jakadancin Amurka tun farkon watan Agusta.

Source: Facebook
Rahoton Visas News y nuna cewa an sauya ko kuma soke wasu alƙawuran da aka riga aka tsara da masu neman bizar, yayin da hukumomin kasar ke gudanar da wani sabon tsari na horas da jami'ansu.
Dalilin dakatar da bizar Amurka
Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce matakin na da alaka da tabbatar da cewa jami'an da ke tantance masu neman biza suna da cikakkiyar kwarewar da za su duba kowanne mutum cikin tsanaki.
An ce an tsara karin horon ne domin tabbatar da cewa jami'an ofisoshin jakadanci suna iya tantance masu neman bizar cikin cikakken bincike da kuma amfani da tsari iri daya.
Hukumomin Amurka sun bayyana cewa daya daga cikin manufofin sabon tsarin shi ne hana masu samun bizar shige da fice zama masu dogaro da tallafin jama'a na gwamnatin kasar.
Wasu daga cikin masu neman bizar da aka riga aka tsara musu ranar da za a masu tambayoyi sun samu sakonnin imel da ke sanar da su cewa an soke alƙawuransu.
An ce za a sake sanar da wadanda abin ya shafa sabbin ranaku, amma har yanzu ba a bayyana lokacin da za a sake tsara hakan ba.

Source: Getty Images
Trump ya kara tsaurara okoki
CNN ta wallafa cewa sabon matakin wani bangare ne na yunkurin gwamnatin Trump na kara tsaurara dokokin shige da fice, wanda ya shafi masu shiga kasar bisa doka da kuma wadanda ke kasar ba tare da takardun izini ba.
Hakan na zuwa ne kwana daya bayan gwamnatin Amurka ta sanar da shirinta na soke bizar wasu masu neman mafaka da suka fara shiga kasar da bizar yawon bude ido ko ta kasuwanci.
Amurka na horas da sojojin Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar sojin Amurka ta fara horas da sojojin Najeriya kan amfani da jirage marasa matuka da sauran dabarun aikin soja.
Horarwar da ake gudanarwa a wani sansanin hadin gwiwa da ke jihar Bauchi ta shafi dabarun kula da sojojin da suka samu raunuka a fagen daga da kuma inganta kwarewar jami'an rundunar.
Rundunar AFRICOM ta ce shirin ya kuma kunshi horaswa kan amfani da makamai, dabarun boye kai, kula da ruwa, gano da kawar da abubuwan fashewa da sauransu.
Asali: Legit.ng

