A karshe, an Gano Wanda Ya Kashe Mawakin Duniya Tupac Shakur

A karshe, an Gano Wanda Ya Kashe Mawakin Duniya Tupac Shakur

  • An samu tsohon shugaban wata ƙungiyar daba, Duane “Keffe D” Davis, da laifin shirya kisan mawakin rap, Tupac Shakur, bayan kusan shekaru 30
  • Alƙalan kotu sun same shi da laifin kisa da makami mai haɗari dangane da harin da aka kai wa Shakur a wani harbin mota a Las Vegas a 1996
  • Davis mai shekaru 63 ya bayyana a kotun Las Vegas cikin baƙar kwat, inda ya saurari hukuncin, kafin daga bisani ya bayyana cewa zai ɗaukaka ƙara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Las Vegas – An samu tsohon shugaban ƙungiyar 'yan daba, Duane “Keffe D” Davis, da laifin shirya kisan fitaccen mawakin rap na Amurka, Tupac Shakur.

Shakur ya mutu ne sakamakon harbin bindiga da aka yi masa daga wata mota yayin da yake cikin wata mota a Las Vegas a ranar 7 ga Satumba, 1996.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace shugaban APC a Kano bayan kai kazamin hari

Duane “Keffe D” Davis da Tupac Shakur
Duane “Keffe D” Davis a hagu da Tupac Shakur a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

BBC ta wallafa cewa hukuncin ya zama na farko da aka samu a shari’ar kisan Shakur, wadda ta kasance ɗaya daga cikin shahararrun shari’o’in kisan da suka daɗe ba a warware su ba a Amurka.

Davis ya ce zai ɗaukaka ƙara

Bayan an karanta hukuncin a ranar Litinin, Davis ya bayyana cewa zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun.

A lokacin shari’ar, kotu ta saurari wani faifan hirar da ’yan sanda suka yi da Davis a sirrance a 2008, inda ya bayyana cewa yana cikin motar da aka yi harbin daga cikinta.

Rahoton Al Jazeera ya nuna cewa Davis ya ce shi da kansa bai harba harsasan da suka kashe Shakur ba.

Masu gabatar da ƙara sun ce duk da cewa Davis bai harba bindigar ba, shi ne ya ba da umarnin harin tare da samar da bindigar da ɗan’uwansa, Orlando Anderson, ya yi amfani da ita wajen harbin mawakin.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan da ake zargi da shirya wa Tinubu juyin mulki ya fita a APC

Anderson ya mutu a wani harbin daban a 1998, bayan ya musanta cewa yana da hannu a kisan Shakur.

Mawakin Amurka, Tupac Shakur
Tupac Shakur kafin a kashe shi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yadda aka kashe Tupac

Masu gabatar da ƙara sun ce Davis ya shirya harin ne domin ɗaukar fansa bayan Anderson ya yi faɗa da Shakur da mutanensa a Las Vegas, sa’o’i kaɗan kafin kisan.

Kisan Shakur ya faru ne a lokacin da ake fama da tsananin hamayya tsakanin mawakan rap na yankin Gabas da Yamma na Amurka, tare da rikicin ƙungiyoyin Bloods da Crips da suka yi tasiri sosai a duniyar hip-hop.

Shakur yana da shekaru 25 a lokacin da aka kashe shi, a daidai lokacin da yake kan ganiyar shahararsa a matsayin ɗaya daga cikin mawakan rap da suka fi yin tasiri.

Ɗaya daga cikin muhimman hujjojin da aka gabatar a shari’ar shi ne furucin Davis da kansa, wanda ya sha bayyana a bainar jama’a cewa yana cikin farar motar Cadillac da aka yi amfani da ita wajen kai harin.

Sojan Amurka ya yi murabus

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban sojojin kasa na Amurka, Dan Driscoll, ya yi murabus bayan watanni ana samun rashin jituwa tsakaninsa da Pete Hegseth.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da 'yan bindiga suka hallaka shugaban APC a Kano

Wata majiya ta shaida cewa Driscoll ya nuna damuwarsa kan sauye-sauyen da ake shirin yi wa rundunar sojojin kasa da kuma shirye-shiryen ta na yaki.

Sai dai wasu rahpotanni sun nuna cewa har yanzu ba a bayyana ko Fadar White House ta amince da murabus din Driscoll ba ko kuma akwai matakin da za ta dauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng