'Shaiɗanu ne Ku': Iran Ta Fusata da Amurka Ta Kai Hari kan Masu Bikin Aure

'Shaiɗanu ne Ku': Iran Ta Fusata da Amurka Ta Kai Hari kan Masu Bikin Aure

  • Babban mai shiga yarjejeniyar Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya caccaki kasar Amurka yayin da ake yaki tsakanin kasashen biyu
  • Ghalibaf ya kira Amurka “Shaidan” bayan wani hari kan bikin aure da ya kashe mutane huɗu a kudancin Iran
  • Ya ce harin ya kashe yara tare da iyalansu, yayin da ya danganta lamarin da wasu hare-haren da suka kashe mutane a Iran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Babban mai shiga yarjejeniyar Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya dura kan Amurka bayan hari a Iran.

Ghalibaf ya kira Amurka “Shaidan” a ranar Laraba, bayan wani hari da aka kai kan bikin aure a kudancin ƙasar.

Amurka ta kai hari kan masu biki a Iran
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Imam Mojtaba Khamenei, Donald J Trump.
Source: Facebook

Akalla mutane huɗu ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata a wani hari da aka kai cikin dare kan bikin auren da aka gudanar a Kuhestak, kudancin Iran, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

Bashin biliyoyi ya taru a kan Kiyosaki da ke koya wa mutane dabarun yin kudi

Yadda harin Amurka ya hallaka yan Iran

Ghalibaf ya ce harin ya yi sanadin mutuwar “yara tare da iyalansu”, inda ya kuma ambaci wasu munanan hare-hare da suka faru a Iran a farkon yakin Gabas ta Tsakiya.

Daga cikin hare-haren da ya ambata akwai wanda aka kai kan wata makaranta da ke Minab, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane.

Ghalibaf ya ce:

“Idan wata ƙasa tana aiki kamar Shaidan, tana zaɓar wuraren hari kamar Shaidan, kuma tana kashe mutane kamar Shaidan, to Shaidan ce. Kuma idan tana kare ƙaramin Shaidan da ke yin haka, to ita ce Babban Shaidan.”

Kalmar “Shaidan” dai Ruhollah Khomeini, wanda ya kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ne ya fara amfani da ita a shekarar 1979 wajen kiran Amurka, kuma shugabannin Iran da suka biyo baya sun ci gaba da amfani da ita.

Amurka ta kai har kan masu biki a Iran
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Harin ramuwar gayya da Iran ta yi

Iran ta mayar da martani kan harin bikin auren ta hanyar ƙaddamar da hare-haren jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami kan sansanonin sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Iran ta kashe sojojin Amurka da dama da ta kai masu jerin hare hare

Hare-haren na Iran sun shafi sansanonin Amurka da ke Bahrain, Kuwait, Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma yankin Kurdistan na Iraki.

Sojojin Amurka ba su yi magana kai tsaye kan harin da aka kai bikin auren ba wanda ya yi ajalin mutane da dama, kamar yadda Tribune ta ce.

Mai magana da yawun Rundunar Sojin Amurka ta Tsakiyar Ƙasa, CENTCOM, Tim Hawkins, ya ce: “Sojojin Amurka ba sa kai hari kan fararen hula, sabanin IRGC,” yana nufin Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran.

Iran ta yaba wa shugaba Putin

An ji cewa Shugaban Iran Masud Pezeshkian ya gode wa Vladimir Putin kan goyon bayan Moscow ga Tehran yayin yaki da Amurka.

Pezeshkian ya ce alakar Iran da Rasha ta kasance mai muhimmanci, yana mai cewa kasashen za su hada kai wajen yaki da danniya.

Putin ya tabbatar da goyon bayan Rasha ga al’ummar Iran, tare da cewa Moscow za ta ci gaba da huldar tattalin arziki da kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.