Gwamnatin tarayya ta sake neman sabon bashin Dala biliyan $1.2 daga ƙasar Brazil

Gwamnatin tarayya ta sake neman sabon bashin Dala biliyan $1.2 daga ƙasar Brazil

- Ministar kudi, zainab Ahmed, ta ce Najeriya ta nemi sabon basshin Dalar Amurka biliyan biyu daga kasar Brazil

- Zainab ta ce gwamnatin tarayya za ta ciyo bashin kudaden ne domin farfado da masana'antun cikin gida

- 'Yan Najeriya da dama na korafin cewa gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Buhari ta na tarawa Najeriya dumbin basuka

Gwamnatin na shirin rancen ƙuɗi kimanin Dala biliyan 1.2 daga ƙasar Braziƙ don bunƙasa harkar noma.

An turawa majalisa kudiri don ta sahale a ciyo bashin daga kasar Brazil.

Ministar kuɗi, kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed, ce ta bayyana hakan jim kaɗan bayan ta bayyana a gaban kwamitin kuɗi na majalisar wakilai a Abuja ranar Talata don kare kasafin kuɗin ma'aikatar ta.

Ministar ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta turawa majalisa kudirin neman yarjewarta domin karɓo bashin kudaden daga kasar Brazil.

Zainab Ahmad tace gwamnatin tarayya zata mallaki hekta dubu ɗari 100,000 na gona a kowacce jiha don noman abinci.

KARANTA: Da izinin gwamnati sojojin Amurka suka kai hari kan 'yan bindiga a arewacin Nigeria - Minista

Inda ta ƙara da cewa za'a yi titunan da zasu sauƙaƙa wajen tafiyar da kayayyakin gona don rage yawan asarar da manoma keyi bayan girbe amfanin gona.

Gwamnatin tarayya ta sake neman sabon bashin Dala biliyan $1.2 daga ƙasar Brazil
Shugaba Buhari da Boss Mustapha yayin zaman FEC @NGRpresident
Asali: Twitter

Shugaban kwamitin ya Mr James Feleke ya tambayi Zainab Ahmad game da yadda tsarin yake.

Da take bashi amsa, Zainab Ahmad ta ce; "za mu yi amfani da bashin don inganta masana'antu da muke dasu.

KARANTA: Kano: Mijina ya na tilasta min akan lallai sai na bashi damar shan jinin al'adata - Matar aure a gaban kotu

"Ina neman amincewarku don karɓo bashi da muke kira Green Imperative Programme, wanda ya kai kimanin Dala biliyan $1.2.

"Tsari ne wanda zai taimaki harkar noma tun daga Kayan aiki, nomawa, sarrafawa da kuma siyarwa.

"Tsari ne da za'a bawa ƴan kasuwa da manoma bashi don sayen motocin noma da sauran kayan aikin shuke-shuke da kuma yin noma."

A ranar Litinin ne Legit.ng ta rawaito cewa Najeriya ta ƙara faɗawa tsilla-tsilla sakamakon sake faɗuwar farashin ɗanyen man fetur a kasuwar duniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel