Putin Ya kai Hari da Shirga Shirgan Makamai da Amurka Ta Ce Ta Ja Kunnen Shi

Putin Ya kai Hari da Shirga Shirgan Makamai da Amurka Ta Ce Ta Ja Kunnen Shi

  • Rasha ta gudanar da gwajin makami mai linzami mai cin dogon zango (ICBM) wanda zai iya ɗaukar makamin nukiliya ziyarar wakilin Amurka
  • Rahotanni sun ce gwajin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takun saka tsakanin Rasha da ƙasashen Yammacin duniya
  • Ma'aikatar tsaron Rasha ta wallafa hotunan harba makamin, lamarin da ke ƙara ɗaukar hankali kan ƙarfin makaman da ta mallaka a halin yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Rassia - Ma'aikatar tsaron Rasha ta sanar da gwajin babban makaminta bayan ziyarar John Ratcliffe zuwa Moscow, inda aka ce tattaunawarsa da jami'an Rasha ta mayar da hankali kan yaƙin Ukraine da alaƙar Rasha da ƙasashen NATO.

Rahotanni sun bayyana cewa ziyarar shugaban CIA na Amurka na iya kasancewa da alaƙa da ƙoƙarin Amurka na gargadin Moscow kan duk wani yunƙurin kai hari ga ƙasashen ƙungiyar NATO.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Tinubu ya shigar da kara kotun Amurka kan zargin da ake masa

Vladimir Putin na kasar Rasha
Vladimir Putin da wani waje da ya kai hari Ukraine. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sky News ta rahoto cewa Ratcliffe ya gargadi takwaransa na Rasha cewa bai kamata Moscow ta ƙara tsananta rikicin da Amurka da ƙawayenta na NATO ba.

An gwada makamin Rasha

A bayan wannan ziyarar ne Ma'aikatar Tsaron Rasha ta sanar da gwajin wani makami mai linzami mai cin dogon zango, ICBM, wanda zai iya ɗaukar makamin nukiliya.

Hotunan da ma'aikatar ta wallafa a yanar gizo sun nuna abin da ta ce harba makamin daga Plesetsk Cosmodrome, wani sansanin harba makamai da ke Arewa maso Yammacin Rasha.

Wannan nau'in makami na daga cikin makaman da ake iya amfani da su wajen kai hari zuwa nesa, ciki har da tsakanin nahiyoyi.

Putin ya kai hari Ukraine

A wani labarin kuma, akalla mutane 37 sun mutu sakamakon wani harin jiragen yaƙi marasa matuƙa da Rasha ta kai da daddare kan wani wurin ajiyar harsasai da ke kusa da Kyiv, babban birnin Ukraine.

Kara karanta wannan

Sojoji sun rutsa yan ta'adda masu karɓar kudin fansa a jihar Kebbi

Gwamnan yankin Kyiv, Tymur Tkachenko, ya tabbatar da adadin waɗanda suka mutu a ranar Asabar, yana mai cewa jami'an ceto da sauran hukumomin da abin ya shafa na ci gaba da aikin kwashe mutanen da kuma bincike a wurin.

Rahoton Al Jazeera ya ce ce manyan fashe-fashe sun biyo bayan harin da aka kai kan wurin ajiyar makamai a garin Myla, kusa da yankunan yammacin Kyiv.

Volodymyr Zelenskyy
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Akalla gine-ginen gidaje 50 ne suka lalace, yayin da gobara mai girma ta bazu zuwa wasu gidaje da wani gidan abinci. An kuma kwashe kusan mutane 400 daga yankin da harin ya shafa.

Daga cikin mutanen da suka mutu har da Taras Didych, magajin garin Dmytrivska, yayin da aka kuma samu mutane da dama da suka jikkata.

Ambaliya ta yi barna a Nepal

A wani labarin, mun ruwaito cewa ambaliyar ruwa mai ƙarfi da ta afku a yankunan Nepal da Tibet na China ta yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane.

Rahotanni sun bayyana cewa masu aikin ceto a ƙasashen biyu sun ci gaba da neman mutanen da suka ɓace bayan wata babbar ambaliyar ruwa mai ɗauke da laka da tarkace.

A Nepal, hukumomi sun ce sama da mutane 2,400 ne ba a iya samun labarinsu ba, yayin da daruruwan ma'aikatan kamfanonin samar da wutar lantarki suka bata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng