Matakin da Amurka Ta Dauka Ya Jawo Matsala a Iran, Mutane Sun Fara Ji a Jikinsu

Matakin da Amurka Ta Dauka Ya Jawo Matsala a Iran, Mutane Sun Fara Ji a Jikinsu

  • Iran ta kasa shigo da isasshen man fetur saboda abin da wani babban jami’i ya bayyana a matsayin killace tashoshin jiragen ruwan kasar da Amurka ta yi
  • Jama’a a Iran sun fara yin dogayen layuka a gidajen mai yayin da yaƙin Amurka da Iran ke ƙara jefa tattalin arzikin Tehran cikin matsin lamba.
  • Hanyoyin jigilar man fetur ta mashigin tekun Hormuz sun ragu sosai, daga kusan ganga miliyan 20 zuwa miliyan biyar a rana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Iran ta kasa shigo da isasshen man fetur domin cike gibin da ƙarancin samar da man a cikin gida ya haifar.

Iran ta kasa shigo da man fetur din ne saboda abin da wani babban jami’in ƙasar ya bayyana a matsayin killace tashoshin jiragen ruwa kasar da Amurka ta yi.

Kara karanta wannan

Ba irin na baya ba ne"; Amaechi ya fayyace shirin Atiku na dawo da tallafin fetur

An fara samun matsala a Iran
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: @drpezeshkian
Source: Twitter

Tashar RTE ta ce kamfanin dillancin labarai na ƙasar Iran, IRNA, ya ruwaito Mataimakin Shugaban Ƙasar Iran, Mohammad Jafar Ghaempanah, ya bayyana hakan.

Mohammad Jafar Ghaempanah ya bayyana cewa samar da man fetur a cikin gida bai wadatar ba, yayin da killacen tashoshin Amurka ta yi ya hana ƙasar shigo da man daga waje.

Ya bayyana hakan ne ranar Laraba, yayin da 'yan Iran suka fara yin dogayen layuka a gidajen mai a wasu sassan ƙasar.

An fara tattauna batun rabon mai

Matsalar ta ƙara tsananta yayin da yaƙin da ake tsakanin Iran da Amurka ke ƙara shafar tattalin arzikin Tehran.

A ranar Litinin, shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasar Iran, Mohsen Haji-Mirzaei, ya ce za a sake duba tsarin rabon man fetur, amma bai bayyana abin da za a sauya ba.

Yaƙin Iran da Amurka ya ɓarke ne ranar 28 ga Fabrairu. Tun daga lokacin ne Tehran ta karɓi iko da mashigin tekun Hormuz mai matuƙar muhimmanci, yayin da Washington ta killace tashoshin ruwa a matsayin matakin mayar da martani.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta sake gano lam'a a shirin Atiku na dawo da tallafin fetur

Jami’in Iran ya soki tsarin tallafin mai

Ghaempanah ya kuma soki yadda ake rarraba man fetur mai tsananin tallafi a Iran, yana cewa tsarin na yanzu ba ya yin adalci wajen rabon tallafin.

Ya ce mutanen da suka mallaki motoci da dama ne suka fi cin gajiyar tallafin, yayin da waɗanda ba su da motoci ba sa samun irin wannan fa’ida.

“Rarraba man fetur a ƙasar ba ya daidaita. Masu motocin da yawa suna cin gajiyar tallafin, sabanin waɗanda ba su da mota,” in ji shi.
An fara samun matsala a Iran
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi Hoto: @AbbasAraghchi
Source: Twitter

Iran na daga cikin manyan ƙasashen da ke samar da ɗanyen mai a duniya, kuma tana da daga cikin mafi arha farashin man fetur saboda tsawon shekaru tana kashe makudan kuɗaɗe wajen tallafa wa farashin man.

Saboda haka, duk wani ƙoƙarin sauya tsarin farashin mai na iya zama batu mai matuƙar tasiri a siyasar ƙasar.

Shugaban Iran ya yi kira ga kasashen musulmi

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya yi kira ga ƙasashen Musulmi da su ƙara haɗin kai, tare da yin hadin gwiwa wajen samar da tsaron yankinsu.

Pezeshkian ya ce bai kamata kare Iran ya kasance ana kallonsa a matsayin ƙiyayya ga ƙasashen Musulmi ko maƙwabta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng