Babbar Magana: Ndume Ya Gano Abin da Zai Ci Gaba da ba Tinubu Matsala a Gwamnatinsa
- Ali Ndume ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya kawar da jami’an da ya bayyana a matsayin “kakistocrats” daga gwamnatinsa
- Sanatan na Borno ta Kudu ya ce rashin ƙwarewar wasu jami’ai na haddasa ce-ce-ku-ce da abin kunya ga gwamnatin Tinubu
- Ndume ya yaba wa Tinubu kan dakatar da wasu manyan jami’ai bayan gano wata hukumar bogi, amma ya ce har yanzu akwai sauran matakan da ya kamata a ɗauka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon mai tsawatarwa na Majalisar Dattawa kuma jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Ali Ndume, ya ba Shugaba Bola Tinubu shawara.
Sanata Ndume ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cire wasu jami’ai da yake zargin rashin ƙwarewarsu na kawo matsaloli ga gwamnatinsa.

Source: Facebook
Ndume ya yi wannan kira ne ranar Laraba, 26 ga watan Agustan 2026 yayin wata hira da gidan talabijin na Arise Tv a shirin Prime Time.
Ndume ya gano baragurbi a gwamnatin Tinubu
Sanatan na Borno ta Kudu ya yi amfani da kalmar “kakistrocrats”, wadda ke nufin tsarin mulki ko shugabanci da mafiya ƙarancin ƙwarewa, rashin cancanta ko masu aikata rashawa suka mamaye.
Ya ce abubuwan da suka faru kwanan nan, ciki har da gano wata hukumar gwamnati da ake zargin ta bogi ce, sun tabbatar da damuwarsa game da yadda wasu jami’ai ke gudanar da ayyukansu.
“Tuni an tabbatar da abin da nake cewa, cewa damuwata ita ce shugaban ƙasa yana da ‘kakistrocrats’ da yawa da suka mamaye fadar shugaban ƙasa,” in ji Ndume.
“Suna ci gaba da jefa gwamnatin cikin matsala”
Ndume ya ce idan Shugaba Tinubu bai ɗauki mataki kan jami’an da bai ganin sun cancanta ba, za su ci gaba da jefa gwamnatin cikin matsaloli da abin kunya.
“Ina nan kan matsayata cewa matuƙar bai yi wani abu a kan wannan ba, za su ci gaba da jefa shi cikin matsala,” in ji shi.
Ya kawo misalin wata hukumar da ake zargin ba ta da ingantaccen tushe, wadda ta yi aiki har ta samu ofishi a cikin harabar ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.
“Ka yi tunanin cewa yanzu abin ya zama sananne a Najeriya; muna da wata hukumar bogi da ta yi aiki har ta samu ofishi, kuma ba su sani ba,” in ji Ndume.
Ndume ya yaba wa Tinubu, amma ya ce a dauki mataki
Ndume ya yaba wa Tinubu saboda matakin da ya ɗauka kan lamarin, musamman dakatar da wasu manyan jami’an gwamnati.
Sai dai ya tambayi dalilin da ya sa shugaban ƙasar bai ɗauki wasu matakan da ya kamata ba domin magance matsalar gaba ɗaya.
“Ina yaba wa shugaban ƙasa. Shi ya sa nake dagewa cewa da yana da ƙwararrun mutane a kusa da shi, da duk wannan rikici da abin kunya ba su faru ba,” in ji shi.
Ndume ya ƙara da cewa har yanzu bai fahimci dalilin da ya sa shugaban ƙasar bai ɗauki matakin da ya dace kan lamarin ba, yana mai cewa akwai buƙatar sake duba waɗanda ke da alhakin gudanar da wasu muhimman ayyuka a gwamnatin.

Source: Facebook
Mutanen da suka taimaki Ndume a APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Mohammed Ali Ndume ya bayyana mutanen da suka taimaka masa wajen sake samun tikitin jam'iyyar APC.
Ali Ndume ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, da uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, sun taimaka masa.
Asali: Legit.ng


