Cikin Trump Ya Dura Ruwa, Ya Hango Barazanar Tsige Shi a Amurka

Cikin Trump Ya Dura Ruwa, Ya Hango Barazanar Tsige Shi a Amurka

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargadin cewa za a tsige shi daga mukaminsa idan jam'iyyar Republican ta rasa iko da Majalisa a zaben Amurka
  • Trump ya ce idan 'yan Democrat suka karɓi ikon Majalisar Dokokin Amurka, za su yi kokarin rusa manufofin gwamnatinsa tare da mayar da su baya
  • Shugaban Amurkan ya bayyana hakan ne yayin wani gangamin yakin neman zabe a South Carolina, inda ya bukaci magoya bayansa su fito su kada kuri'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington, Amurka – Shugaban Amurka Donald Trump ya yi hasashen cewa za a fara yunkurin tsige shi idan jam'iyyar Republican ta sha kaye a zaben tsakiyar wa'adi da za a gudanar a watan Nuwamba.

Trump ya bayyana hakan ne yayin wani gangamin siyasa a Myrtle Beach da ke South Carolina, inda ya gargadi magoya bayansa cewa za su "rasa komai" idan jam'iyyar Democrat ta karɓi ikon Majalisar Dokokin Amurka.

Kara karanta wannan

'A bar yan Najeriya su yanke hukunci': Bashir Ahmad ya kalubalanci Kwankwaso

Shugaba Donald Trump
Lokacin da Donald Trump ke kamfen a Carolina. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Rahoton Telegraph ya nuna cewa ya ce nasarar Democrat za ta hana gwamnatinsa aiwatar da manufofinta a cikin shekaru biyu na karshe na wa'adinsa.

Donald Trump ya ce za a tsige shi

Trump ya ce idan Republican ta rasa rinjaye a Majalisa, 'yan Democrat za su fara yunkurin tsige shi daga mukaminsa.

Ya ce:

"Za a tsige ni. Za su tsige ni. Ba su ma san dalilin da ya sa za su yi hakan ba."

Trump, mai shekaru 80, shi ne mutum na farko a tarihin Amurka da aka tsige shi sau biyu, kodayake bai rasa kujerar shugaban kasa ba a kowane daga cikin lokutan.

Wasu 'yan majalisar Democrat sun nuna goyon baya ga yiwuwar fara yunkurin tsige Trump a karo na uku, kuma akalla uku daga cikinsu sun gabatar da takardun neman tsige shi tun bayan komawarsa fadar White House a wa'adinsa na biyu.

Trump ya gargadi Republican

Kara karanta wannan

Musulmar Afghaistan Aisha Wahab ta lashe zabe a Amurka

Trump ya ce idan Republican ta sha kaye, abokan hamayyarsa za su rusa manufofin da ya ce gwamnatinsa ta samu nasara a kansu.

Ya bukaci magoya bayansa su fito da yawa domin kada Democrat ta samu damar karɓe ikon Majalisa.

Yahoo News ta rahoto ya ce:

"Idan muka sha kaye, za ku rasa iyakar kasarku, za ku rasa rage haraji, za ku rasa duk abin da muka yi."

Ya yi gargadin cewa idan Democrat ta karɓi iko, haraji zai ƙaru, albashi zai ragu, sannan wasu ayyuka da kasuwanci za su durƙushe.

Shugaba Donald Trump
Donald Trump na magana a wajen taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya nemi a fito zabe

Trump ya kasance yana yakin neman zaben Darline Graham a South Carolina, wadda aka nada Sanata bayan rasuwar dan uwanta, Lindsey Graham.

Graham na neman lashe cikakken wa'adin kujerar, amma ta kasa samun rinjaye a zaben fidda gwani na Republican kai tsaye, lamarin da ya tilasta gudanar da zagayen zabe na biyu.

Trump ya bukaci magoya bayansa na MAGA su dauka kamar shi ne yake takarar zabe domin su fito su kada kuri'a.

Kara karanta wannan

APC, ADC da jam'iyyun da suka bayyana shirinsu na fara yakin neman zaben shugaban kasa

Ya ce:

"Don Allah ku zo ku kada kuri'a."

Kotu ta dakatar da Trump

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata kotun Amurka ta sake kawo cikas ga manufofin gwamnatin Trump kan shige da fice.

Alkalin kotun tarayya, Jeannette Vargas, ta yanke hukuncin cewa dakatar da sarrafa takardun bizar wasu 'yan kasashen waje ta zarce ikon Marco Rubio.

Hukuncin ya cire tushen dokar da aka yi amfani da shi wajen dakatar da bizar bakin haure daga wasu kasashe, ciki har da Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng