Ashe ba Daɗi: Donald Trump Ya Ji Zafin Ƙaƙaba Amurka Sabon Haraji da Aka Yi
- Donald Trump ya sake sukar Canada kan manufofin haraji, yana zargin Ottawa da ƙaƙaba wa manoman Amurka manyan haraji
- Rikicin cinikayya tsakanin Washington da Ottawa ya ƙara tsananta, yayin da Firayimministan Canada Mark Carney ya soki sabbin matakan harajin Amurka
- Canada ta dakatar da tattaunawar cinikayya da Amurka, bayan Washington ta gabatar da wasu buƙatu da Ottawa ta ce ba za ta amince da su ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Shugaban Amurka Donald Trump ya sake sukar kasar Canada kan manufofin cinikayya tsakanisu.
Shugaba Donald Trump ya soki yadda Ottawa ke tafiyar da harkokin kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.

Source: Twitter
Trump ya bayyana cewa Canada tana son cin moriyar kasancewa kusa da Amurka kamar wata jiha, duk da cewa ba ta cikin Amurka, cewar BBC.
Ya kuma zargi gwamnatin Canada da sanya manyan haraji kan kayayyakin amfanin gona daga Amurka, yana cewa manoman ƙasar sun dade suna fuskantar irin waɗannan haraji.
Wannan sabuwar suka ta Trump ta zo ne yayin da rikicin cinikayya tsakanin Amurka da Canada ke ƙara yin zafi, musamman kan batun haraji.
Trump ya bayyana cewa:
“Canada na son fa’idar kasancewa jiha ɗaya, ba tare da kasancewa [jiha] ɗaya ba wacce take muradi."
A nasa bangaren, Firayimministan Canada Mark Carney ya zargi gwamnatin Amurka da amfani da sabbin haraji domin raunana tattalin arzikin Canada tare da haddasa rarrabuwar kai.
Carney ya bayyana matakan Amurka a matsayin kuskure, sannan ya yi alkawarin cewa Canada za ta mayar da martani kan duk wani sabon harajin da Washington ta kakaba.
Ya ce daga ranar 8 ga watan Satumba, Canada za ta iya daukar matakin ramuwar gayya kan matakan harajin Amurka, yayin da tattaunawar cinikayya tsakanin ƙasashen biyu ta tsaya.
Sai dai wakilin cinikayyar Amurka, Jamieson Greer, ya ce Canada ce ta janye daga wata yarjejeniyar da kusan aka kammala, wadda za ta iya rage harajin kayayyakin Canada a kasuwar Amurka.

Kara karanta wannan
Abin boye ya fito: An gano bashi ya yi wa Amurka katutu yayin da ta ke yaki da Iran
Greer ya bayyana cewa matakin Canada ya kawo cikas ga kokarin cimma yarjejeniya da za ta inganta harkokin cinikayya tsakanin Washington da Ottawa, cewar rahoton The Guardian.
Rikicin ya ƙara kunno kai ne bayan Canada ta dakatar da tattaunawa da Amurka saboda wasu sauye-sauye da Washington ta gabatar a cikin shawarwarin cinikayyar ƙasashen biyu.
Rikicin ya ƙara kunno kai ne bayan Canada ta dakatar da tattaunawa da Amurka saboda wasu sauye-sauye da Washington ta gabatar a cikin shawarwarin cinikayyar ƙasashen biyu.
Trump ya lafta wa Najeriya haraji
Mun ba ku labarin Amurka ta sanar da kakaba harajin kashi 12.5 kan kayayyakin da ake shigowa da su daga Najeriya saboda zargin rashin dakile kayayyakin da aka samar da aikin tilas.
Sabon matakin ya shafi kasashe 60, inda Amurka ta ce ba su kafa ko aiwatar da dokokin hana shigo da kayayyakin da aka samar ta hanyar aikin dole ba.
Hukumar Kasuwancin Amurka ta ce matakin na daga cikin kokarin gwamnatin Donald Trump na yaki da amfani da aikin tilas a harkokin kasuwanci na duniya.
Asali: Legit.ng
