An 'Gano' Lokacin da Sakataren Rundunar Sojin Amurka zai Yi Murabus
- Ana sa ran Sakataren Rundunar Sojin Ƙasa ta kasar Amurka, Dan Driscoll, zai bar mukaminsa kafin karshen shekarar 2026, watanni kadan ke nan daga yanzu
- Wani rahoton ya ce Driscoll ya samu rashin jituwa da Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, cikin watannin baya wanda ya dagula alaka tsakaninsu
- Ficewarsa na iya barin rundunar sojin ƙasar ba tare da shugaba da Majalisar Dattawan Amurka ta tabbatar da shi ba a lokacin da Amurka ke yaki da Iran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
United States – Rahotanni sun ce ana sa ran Sakataren Rundunar Sojin Ƙasa ta Amurka, Dan Driscoll, zai sauka daga mukaminsa kafin karshen shekarar nan.
Wannan mataki da zai dauka na zuwa ne bayan shafe watanni yana fuskantar rashin jituwar aiki da Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth.

Source: Facebook
Reuters ta wallafa cewa an samu wannan rahoto ne a ranar Juma’a, 21 ga Agusta, 2026, inda aka ambato wasu mutane da ke da masaniya kan tattaunawar da ake yi kan batun.
Sakataren tsaron Amurka zai yi murabus
BBC Hausa ta wallafa cewa idan Driscoll ya bar mukaminsa, hakan zai sa rundunar sojin ƙasar ta kasance ba tare da wani shugaba da Majalisar Dattawan Amurka ta tabbatar da shi ba.
Haka kuma wannan babban mataki zai zo a daidai lokacin da Amurka ke kokarin kawo karshen yakin da ta fara tare da Isra’ila kusan watanni shida da suka gabata.
Haka kuma, ficewar tasa za ta kara yawan sauye-sauyen da ake samu a matakan shugabanci daban-daban na Ma’aikatar Tsaron Amurka, Pentagon, a wa’adin mulkin Shugaba Donald Trump na biyu.
Ana samun sauyi a gwamnatin Amurka
A watan Afrilu 2026, an kori Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa ta Amurka, Janar Randy George, daga mukaminsa. Haka kuma an samu sauye-sauye a manyan mukaman rundunar sojin ruwa da mataimakin shugaban rundunar sojin sama.

Kara karanta wannan
Abubuwan sani game da yarjejeniyar da aka yi tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya

Source: Facebook
Rahotanni sun bayyana cewa Driscoll da iyalansa sun fice daga gidan da aka tanadar wa Sakataren Rundunar Sojin Ƙasa a lokacin bazara.
Dukkanin wadannan sauye-sauye na zuwa a lokacin da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ke ci gaba da barazana ga kasar Iran game da yakin da ake yi.
Trump na son lallai a kawo karshen yakin amma da dokokin da kasarsa za ta aminta da su, yayin da Iran ta ce za a samu sauki ne idan kowa zai mori yarjejeniyar.
Rikici ya balle tsakanin Amurka da Kanada
A wani labarin, kun ji cewa tattaunawar kasuwanci tsakanin Amurka da Kanada ta rushe a bayan dogon zama, lamarin da ya sake kunna rikicin haraji tsakanin kasashen biyu.
Sababbin harajin kashi 50 kan wasu kayayyakin Kanada da darajarsu ta kai dala biliyan 20 sun fara aiki bayan kasashen sun kasa cimma yarjejeniya Firaministan Kanada, Mark Carney, ya ce kasarsa za ta mayar da martani kan harajin Amurka da irin matakin da Washington ta dauka domin kare 'yan kasuwa Read more:
Asali: Legit.ng
